SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(49)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Da safe kuwa ko da queen ta fito tana ta rara gefe da Mama tana jiran taji ta inda maman zata damko ta ta nuna mata kuskuren da ta aikata,se ta lura kamar ma maman ba ta tata take ba,ta ga cewar maman ma bata ma san me queen take yi ba.se ta ware ita ma ta saki jikin ta ta cigaba da al'amuran ta..
Al'amuran rayuwa suka cigaba da wakana da wanzuwa cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali..
Wani zubin ayi kunci,Wani zubin ai farin ciki,dama haka rayuwa ta kunsa ..
Sannan Maman ta Bata fasa in ta fita taga abu ta siyo ba,haka Kuma Bata fasa dambun siyarwa ba saboda ko ba komai tana son tayi wa queen din kayan kitchen duk kankantar su saboda gori ,duk da tasan Uncle Baba zeyi mata komai,amman duk da haka tana son itama ta yi wani abu a matsayin ta na uwa mahaifiya...
✨❣️✨❣️✨
Wai Ina labarinAlhaji Aabid ne?? Ko Kun manta dashi,Ko kuma Kun hakura da sanin inda yake??
Toh ni ban manta ba,ban Kuma hakura ba,gani Kuma na waiwayo shi zamu ji Yaya rayuwa bayan rabuwa da masoyiya..
A kasa yake a durkushe ruke da kafafun wata dattijuwar mace da ta kasance mahaifiya a gare shi..kuka yake Yana mata magiya da cewar....
Umma dan Allah kiyi hakuri ki yafe mun,wallahi daga wannan karon in shaa Allah baza ki sake kama ni da makamancin hakan ba,amman umma Ina ta sake gaya miki akan cewa Abida ita ce rayuwa ta umma,wallahi nayi duk iya kokarina umma for more than 20 years na kasa hakura da ita umma..
Ina gudun cutar da wayanda Basu ji ba Basu gani bane ba wallahi shiyasa umma..
Kuka sosai Aabid yake yi,a kalla shekaru 50 a duniya amman har a yau ya kasa aure ya kasa rayuwa ya kasa yin komai da rayuwar sa saboda tsananin karfin dafin da soyayyar Abidan tayi mai ga yadda take nukurkusan shi ta taba duk Wani bargo da Kashi da tsoka na jikin shi..
Maman shi kanta a yau kam kuka take mishi da ya kasance magashiyan a kasan dakin asibiti...
Zaman shi haka ya ishe ta,ace mutum ya rayu da fankon soyayya tsahon wannan shekarun,danta kenan shi kenan sarkin alkawari siwidi keman Baban soyayya?
Aure ta nemo masa na wata yarinya Aisha,da sudin goshi da bacin rai sannan Alhaji Aabid ya yarda da batun auren,se dai fa,ko a wasa be taba ganin yarinyar ba,balle har a Kai ga zuwa gun ta zance balle ma balle azo batun fahimtar juna..
Sai Kuma a week din daurin auren nasu ne Kuma ya hau rashin lafiya har da su kwanciya a asibiti..
Mahaifiyar shi da ta San halin da yake ciki,ga matsalar tabuwa da kwakwalwar sa ta samu duk sakamakon soyayyar Abidan ne abun Kuma ya tunzirata..
Kai da aka San matsalar ka,Kuma har Kaci sa'ar samun nutsastsiyar yarinyar da tayi shahadar kura ta amince zata sadaukar da farin cikin ta da rayuwar ta ta aure ka,se ka fara kawo kauli da ba'adi kace ka fasa auren ta?
Shiyasa maman tace "shikenan tunda haka ka zabar wa rayuwar ka,ka dauki alkawarin da ka daukar wa kanka da zuciyar ka da muhimmanci ko?
Toh se ka zauna kayi tayi,lafiya dai taka,Kuma duk Wanda Rai yayi wa dadi a bayan me shi ne,sannan ka sani ni !

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Aktuelle Literaturlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...