SAUYIN RAYUWA (BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

MONDAY, 20TH MARCH,2022.

(6)

_____________

Sun dai Sha mamaki,Dan ma Allah yasa da motar su suka taho,da sunga tijara,Dan Hashim haka ya Sanya wa idon sa kwalli,ko irin barkwanci nan ma be Bada fuskar ayi dashi ba.

Abida dai Kai na cikin mayafi takaici da kunyar duniya ta rufe ta,ya rufo gida bayan su Aisha,Hafcy,Muna,zee da maryam sun tafi.

Ya dawo cikin gida,tun a wannan lokacin dama da sauyin shi ya shigo gidan,Ina irin Bude fuskan amare da angwaye keyi ?? Toh Hashim dai be iya shi ba,haka abida ta ga ba sarki se ubangiji da kanta ta Bude fuskar ta. Tana ta murmushi tana sunne Kai wai ita Amaryar so.

Shi kuwa Hashim ya Wani daure fuska kamar Wanda aka hada su ba auren soyayya sukai ba.

Kwata kwata ba fa irin rawar kafar nan da angwaye keyi na musamman a dare irin wannan na samun muraden zuciyoyin su.

Kai gaba daya se da Abida ta fara tantamar cewa ko dai ba Hashim me Doki ta bane wannan? Dan karankachakaf ya juye daga Wanda ta sani a wayar su ta jiya ma da wannan na gaban ta na yau.

Yana daga zaune ya katse mata Dan guntun tunanin ta yace mata "Abida jeki kiyi sallah kizo ki sameni a daki na"

Wani banbarakwai ta ji abun,Amman ta daure ta tashi.

Cikin rashin kuzari Abida ta yi abunda yace,dama tayi isha'i tun daga gida,Amman se tayi sallah raka'ah biyu tayi Addu'oi ta shafa ta chanja kaya,hijab ta Dora Akan kayan sannan ta tafi dakin nashi da tunani barkatai a ranta.

Tafi minti goma a tsaye ta kasa gaba ta kasa baya,ga wata uwar yunwa da take mamayar cikin ta kamar yayan hanjinta zasu rarrabe gida biyu.

Yo a cikin wannan satin Bata samu zama ba ma bare cin abinci.A dazu Aunty badi'an su take cewa ya kamata taci abinci kafin a kawo ta gidan ta.

Amman Bata samu damar ci ba saboda se faman mata nasiha ake ,kawar ta Aisha tace ai ko Bata ci ba ma ba komai,sa ci tare da Angon ta.

A wannan tunanin tana dai bakin kofar Hashim da yaji Shirun yayi yawa ya taso ya biyo sahu.se gata a kofa.

Hannun ta ya kama yaja zuwa cikin dakin,a bakin gado ya zaunar da ita ,sun dai yi shiru kamar masu azumin magana.kuma kamar wasu bakin juna..

Ita kuwa fargaba da bugun zuciya tare da wata matsananciyar faduwar gaba sun sake yin azama wajen ganin sun sake wawake mata Dan ragowar ruwan da yake cikin ta da karfin ta.

Tana dai ta Jira taga Yan kajin da al'adar ko Wani Ango ta tanadar hadi da kayan Madara masu sanyi,gefe guda lemon roba ko na kwali wato exotic ko su chivita.in masu Hali ne ma wasu harda su ice cream,sedai alamu sun nuna Babu ko wanne daga ciki.

Tabbas Hashim be siyo wata kaza ba bare sauran abebaden gefen .shi dai ya ci tashi ya koshi yasha kayan sanyin sa sannan ya taho.

Hashim dai yayi shiru da bakin shi,ba ko irin tambayar ya gajiyar biki dinnan ,a haka yasa ta kwanta bayan yace tayi Addu'a ,dake me ibadar ce se tayi masu wadata sannan ta kwanta.

Gajiyar biki ta hadu da yunwa da fargaba tare da tausayin Kai,bacci barawo yayi gaba da ita.

A cikin baccin ta taji Malam Hashim me Doki,ba tare da Wani Bata lokaci ba ya gabatar da abunda yake ganin Shine dai dai dashi.

Cikin karfin Hali,da juriya daga Abida komai ya wakana ba ko Tari balle kwarmato.

Abida Bata taba tsintar kanta a Wani hargitsi na sauyin Rayuwa ba kamar na yau.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now