SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(13)
_______________
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Yana shigowa Abida ta lura da yadda yake kallon ta ,se ta dan dauke ido.
A ranta Kuma take sake jaddada wa ranta cewa kamar daddy take ganin shi,Shima Kuma a matsayin yar sa yake kallon ta.
Kau da wannan tunanin tayi daga ranta yayin da ta Mika masa kudin da Baba Tajo ya Bata tare da Mai bayanin cewa Baba Tajo abokin daddyn ta ne sun hadu yaga su Asif shine ya Bata.
Godiya yayi wa baba Tajon da baya gun sannan Kuma yace ..Ashe yata ce ta gaske nima ban sani ba,Allahu Akbar! Allah ya jikan Dan fodio usmanu!"
Dago Kai Abida tayi ta Kalli Uncle Baba Jin yadda ya kira sunan Daddy da abokan sa kan Mai inkiya da shi.
Cewa yayi "Abida Baban ki abokina ne,Kuma abokin Arziki"
Cewa Abida tayi "Allah sarki Uncle Baba.." se ga hawaye yana taruwa a idanun ta.
Cewa yayi "kin tuno da shi ko? Ko da yake Baki ma taba mancewa da ita ba.Allah ya jikan su ya musu rahama"
Ameen Abida ta amsa tana sake gasgasta iKon Allah.ya hada ta da Abokin Baban ta ya taimake ita ,ho Allah gatan bawa ne .
Da haka suka cigaba da tafiya bayan Uncle Baban ya gaya mata Tajo ne ya gaya masa ya ga diyar marigayi Usman.shine shi Kuma ya gane cewa itan dai ce.
Cike da kwarin gwiwa suka cigaba da siyayyar su .Amina da Saudatun komai iri Daya suka Siya.
Abun dai daya ne ,ita Amina ubanta gwaska ne,Amman kwakwalwar ta ce ta Samo mata scholarship din,haka zalika Saudat, mu ma ce ubanta Bai da kudi tunda matsolo ne,amman ita ma Allah yayi ta da kwakwalwar da ta sa ta samu scholarship din.
Se gashi Allah ya rufa musu asiri tashi daya an samu Wanda ya rufin asiri.
Stationary din ma ma'su tsada na Yan gayu aka siyawa Saudatu.
Bayan sun gama siyayyan se da ya Kai Abida har gidan shi suka gaisa da matar ce Me suna Mammy Aisha yake gaya mata cewa yarinyar marigayi ne.
Da fara'ah ta tarbi su Abida.aka gabatar musu da lafiyayyen abinci bayan sunyi sallah.
Ga yunwa da komi,Amman Abida kasa ci tayi,yo ta baro Yan marayun diyan ta a gida da fara da mai,yaushe zata wani iya samun damar cin abinci?
Saudatu ma kin ci tayi,se da Abida tace mata taci sannan fa taci.ai ko abinci ne me dadi ga lafiyyun kaaji ciki ..
Bayan sun gama komi akwai Wani drivern Mammy me suna Malam salis ,shi daddy yasa yaje ya maida su Saudatu gida don shi gidan shi a nan Sultan road yake ..kuzo kuga kuka a gun Amina wai za'a tafi da su Asif din ta .
Tuni hankalin iyayen ya tashi,se Wani ririta ta ake yi ana rarrashin ta .Allah sarki Abunka da wayanda sukai shekaru a kalla talatin da Aure kan su samu su haihu.
Da tsufan su fa suka haihu da yake Allah yayi suna da rabon haihuwar ..
Ba dole a nuna mata soyayya ba,shi yasa fa daddy duk kudin sa yake mata wahalhalu irin su Kai ta shopping,ko park ko komai ma,hatta school shike kaita se malam salis ya dauko ta .Shima ba kullum ba.
Malam salis dama driver din mommy ne,to shi daddy baya taba yadda driver ya tukashi,da yake ya iya tuki tun zamanin samartaka,Kuma har a lokacin nan daddy badai tuki ba.
Toh shi yasa daddy baya kyashin mata komi.
A yanzu ma se shagwabar ta take zuba musu.
Dole suka rarrashe ta ta yi shiru su Abida suka samu suka fito,da yake akwai wadatattiyar tarbiya a tattare da ita.
✨💞✨💞
Bayan sunje gidan su murna a gun Yara ba'a cewa komai.
Dama tun a gidan Uncle Baba Abida ta ce "Baba Dan Allah Ina Neman alfarman Baba salis ya biya da ni ta kasuwar tarauni in zamu wuce .."
Cewa yayi "ba tarauni ba duk inda kike son zuwa ya Kai ki,ya juya ya Kalli Malam salis yace "ga yata nan zaka kaita duk inda take so kaji ko?"
Amsa wa yake cikin farin ciki,saboda uncle Baba Wani irin mutum ne me kirki har yayi over ma..
Ko da ya kawo su Abida gidan da Mammy ta gansu a ranta tace "ko a Ina Kuma ya Samo su"
Se da yace mata Yarinyar Dan fodio usmanu ce da ya'yan ta,sannan ta daina tunanin nata.dama ya gaya mata yadda sukai tun wanchan lokacin .ita ma Mammy se suka Bata sha'awa.
✨
A tarauni kuwa Abida ta sauka ta siyo kajin ta lafiyayyu guda biyu dika dika.sannan ta Siya musu dankali ta Siya Mai sannan lettuce da kayan miya.
Suna Isa gidan ta zaro 2k ta bawa Baba Salis.murna sosoi yayi Yana ta shi mata Albarka,yana tayi wa Yaran ta Addu'a.
Da yake suna tsayawa se Saudatu ta sauka ta kwankwasa gate din.
Su Kuma su Abul dama a kan kaya suke ganin mama Bata dawo ba gidan shiru.
So duk motsi se sun leka.yanzu ma hakan take,sedai suna lekawa suka hango maman su da Yan uwan su.
Murna,haka suka kwashi kayan zuwa ciki .dama sunyi sallah gidan Uncle Baba,se kawai aka hau bubbude kaya gwanin sha'awa kowa yana ta murna.
Ga yar siyayyar da dole uncle Baba ya sa tayi,nan suka Bude kayan Dadi suka ci suna Hira cikin nishadi suna shakar iskar yanci tunda ubansu yayi tafiya.
Bayan sun tattare komi suka ajje,se Zahra ta fara gyaran kayan miya,Abul yana fere dankalin.mama kuwa tana gyaran kaji.
Wato da ta samu kajin nan ta Dora akan gawayin da Saudatun ta hura musu yayi jajur ,se ta yanka Albasa.ga garlic da ginger wannan ma siyo su tayi.
Ta kawo su curry da thyme ta zuba da maggi da gishiri se daddawa.
Ana gama grating kayan miya da watsa su bisa ta Saka Dan ruwa ta maida tukunyar ta ta rufe.
Gefe Daya aka sake daura kasko aka fara soya dankali Dan Suma duk sun Saka hannu a fere .
Zahra ta yanka salad ta wanke shi fes aka tsane shi aka juye shi a roba.
Kai wato in takaice muku da aka gama farfesun nan da dankali suka samu tire aka zuba komai a ciki gefe guda kaza guda daya,gefe guda dankali se gefe daya Shine Salad din.
Wannan hadin naji ana kira da dabge ,haka suka dukufa suka ci abincin su cikin kwanciyar hankali ga dadin da abincin yayi wa ko wannen su daga ciki.
Kamar kullum Abida ta fara tashi ta bar wa Yaran,Amman a wannan karon ba dan babu abincin bane ,kawai saboda wannan dabi'ar ta ce ta Uwa Wanda ba'a taba Kai karshen kwano da ita .
Bayan duka sun gama sukai zaman Hira,A nan ne Proff take cewa "Mama dazu fa Amina cewa tayi in koma gidan su muna zama tare Amman wai se a Basu Asif su ruke shi "
Dariya sukai dukkan su,dan yadda proff ke bada labarin ko baka so ba,se kayi dariya..
Wai har Amina na cewa "Ai mama zata barki ki dawo gidan mu ko? Kuma in kina nan ai zata yarda ta bar mana Asif ko tunda ai su biyu ne ko?"
Dariya su Abida suka ruga mata sosai,Shirme kam me kyau Amina ta zuba dazu.cewar Abul.
Kuma fa she is very smart ,Amman dai a nata ganin za'a bar mata baby daya tunda mu guda biyu gare mu "Maman take gaya tana dariya "
Allah dai ya kyauta.sannan Nima Kuma zan tsaya a nan din nan don wallahi Kai na is messed up ne..
Please share 😀
TBC.........
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Ficción Generallabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...