SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(42)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Ita dai Mama mamakin yadda aka yi har aka Sanya ranar auren Zahra wata biyu masu zuwa ne duk ya dameta yake bata tsoro da har ma da mamaki.
Se kace auren yar tsana,toh ko yar tsanar ce in dai da gatan ta ai yaci a Saka fiye da wata biyu dan a shirya a nutse a harhada mata me za'a harhada,balle yar mutum ,yar mutum din ma yar masu rangwamen karfi ne ,ai suna bukatar lokacin da zasu samu suyi dan abun da zasu iya yi ba a matse ba..
Nabila dai murna ita dasu Asif,Addar su zatayi Aure za suyi biki suma a gidan su,da yake basu taba zuwa biki ba tunda suke se ya zamana se tsalle suke ta zabga wa suna rawar murna.
💞✨💞
Ita kuwa sarauniya Zahra'u gaba daya jikin ta ne ya mutu ta zama kamar wata kankara tsabar sanyin da jikin ta yayi mata..
Tunani ne take tayi Wanda baya da iyaka.wai ace yar itan nan ce har an Saka mata ranar aure, wai Kuma nan da watanni biyu,sautitn me ake haka toh?
Abun daga wasa yana neman zamo wa gaske?
Bata ce bata son ya Sufyan ba,amman Kuma bata taba kawo zaton cewa zasuyi auren nan na gaske ba sannan da wuri haka..sannan ko zasuyi auren gasken bata dai taba gigin kawo auren a kurkusa har haka ba..
Hannun ta ta Sanya ta shafo fuskar ta zuwa Saman kanta hade da juyi daga kwancen da take.
Gaba daya a tsorace take da maganar,shi yasa ma da take jiyo hirarrakin su Nabila da Yan biyu kan maganar auren nata taji wata iriyar damuwar da har se da tasa kuka yazo mata..
Haka ta zauna ta dingi kuka ,kukan ma kukan banza da na wofi..yo ita fa tace tana so 😂
Juyi tayi a kan yar katifar su tare da kifa kanta a kan pillow ta sauke ajiyar zuciya tsabar kukan da ta Sha..
Da sauri kuma dauke da Sallama a bakin Nabila da ta turo kofar dakin su ta shigo kawo wa Addan wayar da ya Sufyan ya kira tayi turus ganin Addan ta na kuka..
Cewa tayi "Adda mene ya sameki?"
Bata ce komai ba,se wasu hawayen suka sake gangaro mata masu matukar dumi ...
Wayar Nabila ta mayar a kunnen ta da taji Ya Sufyan Yana cewa "Dr me ya faru da Addan?"
"Kuka take yi" ta fada a hankali hawaye na silalo mata itan ma..
Kashe wayar yayi ya Kamo hanyar dawowa unguwar dan da ya fita ne ze je ya gaisa da Friend dinsa da yazo yin Wani aiki garin Kano shine ya kira shi yace Mai ya zo gari..
A dole ya juyo Allah ma ya so beyi nisa ba sosai, mintuna 15 suka dauke shi ya iso har kofar gidan..
A lokacin ita Kuma Nabila ta gaya ma Mama Addan na kuka shine ta shiga dakin ta same ta suke magana.
Maganar gaskiya dole ne Zahra ta tsorata, saboda daman mafi akasarin aure na mace in ya tashi har ciwo ake yi musamman irin mu na da da mukai aure da dan ragowar tsohon zamani.
Ba zamanin yanzu ba,few of amare ke wannan ciwon damuwar yin auren..sauran kuwa zo kuga rawar Kai a hau yawon raba kati da sauran shirye shiryen shigewa daga ciki..

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Genel Kurgulabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...