SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(52)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Bayan dogon kuka shabe shabe se Galadima ya fara cigiyar Ahalin Alh Badamasi Dan Sarki.
Nan aka tabbatar masa da wucewar su a safiyar ranar..
Galadima yace "nifa da idanuna na gan shi a gun sadaqan nan"
Aka ce wa Galadima "eh,ai bayan sadaqan ne suka kama hanya"
Shiru Galadima yayi Yama rasa me zaice,shi gashi ya amshi har miliyan dayan Alh Ridwan,sannan yanzu ace sarki ya bar wasiyyar magajin shi,har biyu? Bayan shaidun matan sa da ya Sanar wa??
A dole ba dan yaso ba ya sallami taron da cewa "za suyi binciki Alhaji Badamasi game da sarautar da mahaifin sa ya bar masa "
Haka aka tashi bayan sun koma gida shi dai Galadima ya dauko kudin da Alh Ridwan ya basa ya mayar masa tare da bada hakuri akan yadda abubuwan suka kasance ,domin Basu Isa su murde wannan sarautar ba su bawa Wani,hatta Yan garin sun Fi son Alh Badamasi yayi musu sarki ba Alh Ridwan ba..
Yo shi Alh Ridwan din ma a Ina suka gan shi,shi fa bama a kasar yake Zaune ba fa,kawai kwatsam se kayo tsalle ka shiga gaban yayan ka?
Bayan Galadima ,hakimai da yawa sun mayar wa da Alh Ridwan kudin shi,Suma suka hada masa da hakurin ya amsa ,domin su dai za suyi mubaya'ah..
✨💞✨💞✨💞
Mutan kuzoma sun sauka a gida lafiya sumul .. Alhamdulillah
A gidan Kuma ne Galadima ya kira shi Alh Badamasi ya shaida masa yadda batun bawa kanin shi Ridwan ya lalace .
Nan yake shaida masa cewa "Mai martaba Sarki ya bar wasiyyar cewa Kai ne zaka gaji kujerar shi"
Gaban Alhajin su Sufyan ya fadi.
Yace "Allah ya taimaki Galadima,ai kuwa Baba ya San bana son sarauta kwata kwata,siyasa na zaba Kuma ita nake yi,kuma har yanzu Bata chanja zani ba,ni bana son sarautar nan fa"
Gyaran murya Galadima yayi,Yana hasaso yiyuwar sake amsar wannan kudin na wajen Alh Ridwan,yace "ah toh ai ba damuwa,ayi shawara dai ,tunda akwai damar ka zabi Wanda ze maka madadi ko?"
"Eh,inji Alhaji Badamasi,yace ba komai in shaa Allah "
Cewa Galadima yayi"da ai har ana kokarin nada dan uwan naka se aka bamu wasiyyar "
"Allah sarki " Alh Badamasi yace sannan ya sake cewa.
"toh Allah ya iya mana,ya zaba mana mafi Alheri"
✨💞✨💞
Bayan kwana biyu da yin wannan wayar ta tsakanin Alh Badamasi da Galadima ..
Shiru shiru Alhaji Badamasi be sake waiwayar maganar ba, Galadima kuwa yana zargin Indai Alh Badamasi ne ze iya barwa kanin shi Ridwan sarautar mahaifin nasu..
Ko da Galadima ya sake Kiran Alhaji Badamasi,se yace ya basa lokaci ze kira shi..
Zuwa yayi ya samu matan sa suna Hira a part din Mama,yace "Sannun ku matan Sarkin kuzoma "
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...