SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(12)
_______________
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Bayan Abida ta yaye Saudatu a lokacin ne ta sake tafi maganar makaranta . Baban Abul yaki ,tace islamiyya nan ma yaki se tace toh zata fara Sana'a saboda da ko ba komai zata samu ta rufawa kanta da ya'yan ta asiri se ta zauna ta sake zubawa sarautar Allah ido.
Da yake Allah ba azzalumin sarki bane se Baban Abul ya hadu da tsautsayi,Wani marutu ya fito masa mazaunan sa da gwiwar sa.
Haka fa wannan marurun suka hana shi sukuni suka Hana shi sakat.yayi ta faman cin Uban shi.
Kai ko tafiya ma da kyar yake yi,Kun San kurji a gwiwa ba mutumci ga Wani a chan gun,ga shi Baban Abul ba halin zuwa asibiti tunda baze tafi yana ta tattalewa ba kamar Wani Dan kachiya ,yana kyashi yana komi,dole ya bawa Abida kudi taje ta Siya masa magani.
Kafin ta dawo daga siyo maganin ta tarar da Saudatu ta yayyaga kudin Baban Abul da ya boye a cikin hular shi dake gefen shi a kasa, taci Wanda zata ci ta yaga na yagawa.
Baban Abul kuka da idon sa yake yi, na zafin maruru da ciwon cin mutumcin kudin sa da yar sa tayi masa.
Haba malam,da me ma zaiji ne wai?
Gashi ne Isa ya dake ta ba yana fama da kan shi.
A wannan tsakanin Abida ce ta koma sak matar gida.
Da yake Dan rainin wayo ne shi baze ci mara dadi ba,dole take cefane da kanta sannan ta dafa abinci ya samu yaci tunda ba kafar zuwa cin balangu da tsire a tukubar masu tsire ko abincin restaurant .
A wannan lokacin Wani yanci da Abida ta samu,sannan ga kula da shi da take yi ba tare da kyashi ba,ah toh ita da bata da mugun nufi a ranta?
💞✨💞✨💞
An sake samun shekaru zuwa sanda ciki ya bullu a jikin Abida da Baban Abul yawa Allah ya Isa in tayi tsarin iyalin ba tare da yawun shi ba.
Toh aniyar Baban Abul ta bishi,a Bata tsara ba Allah ya tsara mata ko wace haihu se ta shekara uku zuwa hudu take wata .
Kamar dai yanzu da ta haifi Nabila yar ta fara jajur da ita .
Babu abunda ya chanja daga yadda kuka San rayuwar gidan na Abida ..
Nabila nada shekaru 3 mommy ta rasu sakamakon rashin lafiyar da tayi.
Ba'ai Arba'in din ta ba daddy ma ya fadi sakamakon damuwa da rashin mommy Daman Shima yana da hawan jini se kawai ya yanke jiki Amman shi likitoci sunce wai Cardiac arrest ya samu.
Su Abida sunga tashin hankali ,ace kan ayi Arba'in din mommy daddy ya rasu .hmm Allah kasa mu cika da kyau da Imani .Ameen
Bayan daddy yayi Arba'in aka zo rabon gado.ko da aka raba gado babban yayan su Abida wato Ya yahuza shi ya amshi kason Abida ,dama na Wanda ya Wani kira ta ya Sanar da ita maganar rabon gado.ao ba ta ma San me ake ciki ba.
A tsakanin Yan uwan sukai shawarar bar nata gadon zuwa gaba kadan a ga yadda Hali ze yiyu .
So gadon Abida na gun yayan ta yahuza.
💞✨💞✨
An dawo labarin ..
Se Uncle Baba yace "Se Kuma nake so na dau nauyin transportation din ta,haka ma yayi?"

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Fiksi Umumlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...