(22)

58 8 1
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(22)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

An bani hakuri Kuma na hakura ,Amman gaskiya da nayi fushi,musamman Yan dandalin karatu few mutane ake ganin comments din su,sannan read da yawa . please ku gyara ai ba faduwa a cikin bamu karfin gwiwa ko?

✨💕✨💕✨💕

Isar Mama Abida gidan da take aiki ,inda ake Kiran ta da Iya se kace wata tsohuwa,ko da yake kallon tsohuwa ake mata,macen da har yanzu ko Arba'in Bata Yi ba a duniya,Amman YAU ta sata ta tsofe ,har ana mistake din sunan ta ana ce mata iya.hmm

Isar ta gidan taga Hajiya Rukayya wadda ta kasance uwar gidan Alhaji badamasi wadda dama ita ta dauki Abidan aiki,tana ta faman fada akan cewa Drivern su Abdullahi,da yake matashi ne yana wasa da aiki sa,kullum se ta fito zata fita se ace be karaso ba,wata rana ma se ace be zo ba ?

Gashi inda zata je guri ne matukar muhimmanci,gashi Daman  ta ruga ta makara.

meeting ne na Wani foundation da suke dashi,duk da ba wai nata bane ba,na kawarta ne da ta bude,Amman se ya kasance duk shawarar budewar da za'ai da tsare tsaren komai da ita Hajiya Rukayya Akai.

Dan haka se ta zama Daya daga cikin board members din foundation din, ko ince Assistant din hajiya Aimana kawai

So da yake Hajiya Aimana ta girmewa Hajiya Rukayya da kusan shekaru uku ma ,kenan duk sun manyanta.dan Hajiya Rukayya ma ba'a dade ba yaranta da jikokin ta suka mata surprise birthday,Kuma ko a lokacin tayi 62 years.

Kenan Hajiya Aimana tana da 65 kenan?

Yawwa so Hajiya Aimana ta samu matsalar kafa,tana ta fama se ya zamana Bata cika iya fita ba,da yake abun ya hadu da jikin kiba,ga shekarun tsufa se take zama daga gida,se Haj Rukayya ke tsaye akan komai na foundation din.

Se dai ita ma Haj Aimana tana zama daga gidan ana  zoom meeting da ita.

toh Hajiya Rukayya ita ke tsaye akan foundation din nasu Kai da fata shiyasa yanzu da akace Abdullahi be zo ba abun ya bata haushi.

Ta tsani taga ma'aikaci na wasa da aikin shi.shi kenan shi kullum a be zo ba yake ? In Kuma aka Kore shi se yace an masa ba dai dai ba?..

Gashi kuma duk girman gidan Alhaji badamasi su biyu ne drivers,daga na Alhaji se Abdullahi Wanda nasu ne ita da kishiyar ta.

Ita ma kishiyar me suna Mama Hafsatu,Bata Wani cika fita ba,ita ce Amarya fa,amman Ina irin kasaitattun matan nan masu ji da ado da kwalliya duk da shekarun tsufa sun fara zuwa mata? don a kalla ita ma wuraren shekaru 55 take .

Amman ita Bata fita,ta yarda da cewa komai take so daga gida za'a iya yi mata shi,ko dai tayi order ko Kuma tayi aike.

So mostly yasa Abdullahi ya koma drivern Hajiya Rukayya kawai ita waccen hakima ce .

Sannan Ina irin gidan tsofaffin da suka gama aurar da Yaran su ,suka koma se su kadai kwal?

Toh haka abun yake.

shi Kuma Alhaji badamasi Ina irin Mutanen nan da baya son ihu ko hayaniya?  Shima haka yake .

shiyasa ko jikokin sa basu cika zuwa su Wani dade ba matukar yana gidan,dan in yaji hayaniya kamar ze mutu haka yake ji.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now