SAUYIN RAYUWA (BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

MONDAY, 19TH MARCH,2022.

(5)

___________

Tafiyar su Abul islamiyya Abida ta fara Sana'a,wato tuanani.

BAYA

Bayan sun bar  race course,malam lawan gida ya wuce da Abida Kai tsaye,ta fito daga mota jikin ta yayi sanyi kalau.

A lokaci daya abubuwa biyu  na damun ta,na farko tunanin Mai Doki,na biyu tunanin Abid na ganin yadda ta San cewa Kiri Kiri Bata kyauta masa ba.

Sedai  itama tasan cewa ba laifin ta bane ba,saboda ita a kanta Bata San ma ya akai ta basa number dinta ba,gashi Kuma ta debo ruwan dahuwar kanta da kanta.

Cikin gida ta shiga masu aikin gidan su se sannu da zuwa ake mata,da yake mutum ce me kulawa ga bawa na sama da ita girma ko da me aiki ne ,wannan dalilin yasa kowa yake son Abida a gidan.

Masu aikin gidan da kansu sun San cewa yau ba lafiya ba.

Taje ta gaida mommy sannan tace ta dawo ,mommy na ganin ta tasan ba lafiya,Amman ita Kuma uwa ce mara katsalandan a rayuwar yayan ta matukar ba gani tayi Abu yaci tura ba.

A tarbiyar gidan su Abida duk wata damuwa Allah ake gayawa ita.dalilin da yasa mommy ta Kyale Abida ta tafi ba tare da ta nemi Jin ba'asi ba daga bakin ta.

Kamar da kasa kuwa .Sallah ne Abu na farko da Abida tayi ta gayawa Allah,se Kuma kuka da batasan daga ina yake ba.

Abid ne ya kirata a waya tana dagawa cikin sallama ya amsa mata ,cewa yayi " Yaya aka je gida?"

Tace "Lafiya Lau"
.yace "ya aka tarda mommy na"

Da Dan murmushi me sauti tace "ita ma lafiyan ta kalau.."

Cewa yayi "Alhamdulillah ..Amman Abida Ina San kisan cewa Ina son ki,Ina kaunar ki wallahi Ina Miki so fiye da yadda kike zato,Ina Miki son da nasan ba abunda bazan iya yi Miki ba ,Dan Allah karki raba damar da kika bani,ki fara bari kiga iya gudun ruwana kan ki rana mun soyayyar ki Dan Allah..."

Tabbas jikin Abida yayi sanyi,a zaune take a sallaya dama,take wasu sabbin siraran hawaye suka sake zubo mata a idanun ta ,a dai dai lokacin kuma Mai Doki ya fara kira,kira ba kakkautawa .Abid naji yayi shiru ya cigaba da kafa gwamnatin shi.

Amman Kuma alkawarin yayi wa Kansa cewa duk abunda Abida take so baze taba hanata ba,a yanzu in tace zata daga wayar Mai Doki,ze barta.amman shi Kuma baze ce ta daga ba..

Kamar daga sama Abida tace .."Abidina,sorry please zan kiraka Bai bar kira ba har yanzu"

Cike da karsashi da Kara mata karfin gwiwa yace "Okay toh sekin kira ni"

Ya kashe waya,ita Kuma ta daga ta Hashim Mai Doki

Tana daga wa ya fashe mata da kuka wallahi ba Abida ba ko mommy Abida Hashim yayi wa wannan makircin se ta fola.balke wata Abida,tuna fa ta rikice ta rasa yadda zatayi,se hakuri take bashi kuka yana yi yana kalamen soyayya irin Wanda Abid be taba biya mata su ba.

Hashim yace "Wallahi baby ,Allah in har ban ganki ba yau mutuwar zanyi,wallahi tallahi in ban ganki ba bazan sake kwana a duniya ba"

Shege Hashim,ai yasan bazata Hana sa ganin ta ba,shi yasa ya hakikan ce yake ta rantse rantse ,ilai kuwa se gashi ta bashi Address din gidan su.an idar da maghrib kenan yace yazo.

Hashim yadai tsaya a kofar gidan,Amman se yaga kamar ba daga nan zata fito ba,yaga gida Aljannar duniya Dan bala'i dare kamar rana se abubwa yake gani suna Wal Wal kamar gwal Dan kyalli.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now