SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(45)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Yau ta kasance talata,wanda ya zama saura kwana uku kenan daurin auren Zahra da Sufyan..
Waya ce makale a kunnen ta tana zaune ta takure kanta a bango saboda tsananin faduwar gaba da damuwar da ke damun ta a kwanakin nan duk ta bi ta rasa sukunin ta,sannan kuma ta rasa me yasa haka..
Se da ma ta samu mama da maganar, ta gaya mata yawan faduwar gaban da take fama dashi a wannan tsukun,ga mafarkai dake zuwan mata a bacci Wanda take mance me ya faru a a mafarkin da ta tashi,maman tace mata ba wani abu bane ba dama hakan na faruwa a rayuwar dan adam.
Tace mata kowa nayin irin wannan abun,yanayi ne na jiki da jini da ruhi,amman InshaAllah in ta dage da Addu'a koma mene Allah ze shiga al'amuran nata..
Abun ma gaba daya tausai ya bawa maman dan har se da tayi kwalla a bayan idon Zahran saboda tausayin rayuwar da Zahran zata fara a yanzu..
✨💞
Ku tsaya.wato shi fa Aure da kuje ji da gani ba karamin abu bane, rahamar sa da falalar sa yawa gareta,Kuma har in mace tayi aure ko za'a mata aure ba wai daurin bane kawai,hatta a jiki da ruhi se ta ji shi,Kuma ko ta sani ko bata sani ba..
Ga dai Zahra nan ita da bata ma san da maganar auren nata ba,amman impact din abun ya dame ta Kuma ya taba ta subconsciously..
Toh mu dai Yan biki, ko amarya ta damu,ko taki damuwa mu dai se mun daura,in da baki ce kina so ba za'a baki shi dole ne?
Da zaki zo kina raina mana wayo kina wasu koke koken wofi??
Chan kisan inda zaki yi wannan kukan naki,amman ba a nan ba kam..
"Yanzu mene wani abun damuwa Fatima? ,ku da ran Friday ma zaku yi tafiyar ku minjibir park ku bar mu" ya fada cikin son kwantar mata da hankali tare da kashe murya alamun rarrashi.
Turo bakin ta sake yi sannan tace"Toh muje tare man,hadda ma Maman mu"
"Ai matsalar gurin Yara ne banda manya Fatima "
"Ni dai gaskiya bana son naje,na fasa zuwa,nafi son a tafi da Maman mu ita ma ta gano park din"
Cewa yayi "ohh masu mama,naga maman ma tafi so na akan ki da kike mana iyayi"
"Ba wani nan,ni tafi so" ta fada cike da kaguwa domin kiris ya rage ta fara sana'ar ta da ba salary wato kuka..
Murmushi yayi kafin yace "toh naji,tafi son ki,nima Kuma Ina son ki,yar gatan Mama da Yaya"
"Ga ma su Mama again "
ta fada da murnar ta domin ta San yadda su maman suke son ta,dan har gaisawa take dasu a waya in Sufyan yaje gun su se ya kirata ya basu su gaisa..sosai suke sake mata wallahi,wai dan ma zahran sarauniyar kunya ce..
Ba karamin son Zahran su maman suke ba duka su biyun kamar su hadiye ta ko su maidata cikin cikin su,Zahra ta zama shalelen kowa..
"Toh kin gani ma",yace yana gyara zaman labcoat din jikin sa dan yana asibiti ne daman..
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...