SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(8)

_______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

A hanyar islamiyya kuwa yayan Albarka ne ,da yake islamiyyar ba Nisa gare ta ba har sun Kara sa .

Kamar hadin Baki se ma Ustazu izzuddeen a waje,Kun San sabbin malamai da bin ka'idoji da feleke,se gashi yana tsaron Yan latti,ba wai fa sun makara bane ba.

Kawai dai tun wuri ya fara nashi, se Nemo laifin dalibai yake yi,gashi ya make murya ,haba me su Abul zaauyi ba dariya,Dan dama hirar shi suke ta yi suna dariya suna zuwa ko se gashi.

Cikin sa'a Kuma yadda proff take geada yadda yake maganar haka yake yi din.

Suna kumshe dariya suka kada suka shige cikin makaranta sukai Alwala Akai sallah sannan kowa ya wuce Aji.

A gida kuwa ganin ba sarki se Allah yasa Abida ta tashi zaune ta dawo tuananin yadda zata sama wa yaranta  abinci kan su shigo.

Ta Kai goro ta Kai Mari Amma Bata samu hanya ba,wannan mugun hali na Baban Abul ace wai duk fadi da girman gidan nan se a nemi Dan abun kaiwa Baki Babu? Kai jama'a

Dake Allah na sane da dukkan bayin sa ,se gashi tayi bakuwa,ita din wadda tazo yar uwar Hashim ce daga bangaren Alhaji.sunan ta mama Saffiyya .

Tazo musu da tsarabar awara soyayya tana ta tashin tururi dan tasan Abida na son awara matuka.

A ran Abida murna take kamar ta san cewa basu yi sanwa ba ..

Da fara'ah Abida ta yunkura ta tashi ta tarbe ta tana mata maraba,amsar kayan hannun ta tayi cikin Jin dadi dan tasan cewa ko ba komai kwana biyu muguwar ka'idar gidan su se ta Kau..

A tabarmar dake shimfide suka yada zango,nan Abida ta gaishe da mama Safiya cikin Jin dadin ganin ta tare da tamabayar iyalen ta ,dake cousin din su Hashim ce ta bangaren Baban shi,Amman Kuma ba yarinya bace dan akwai kimanin shekaru goma a tsakanin ta da Hashim din.

Hira suke cikin aminci bayan Abida ta kawo mata ruwa ta Sha..kunyar duniya ta hadu ma Abida ,tunda mama safiyar takan zo musu,sedai duk sanda zata zo cikin iKon Allah se kuga Babu abinci a ajiye ,abun dai ba Dadi Sam,Dan se aga kamar Abidan ce bata Dora wa .Dan ma dai! Mama Safiya ta San halin Hashim da Abidan keta kokarin boyewa ..

Bayan dogon nuku nuku da kunbiya kunbiya se Abida ta samu dai tace "Mama kiyi hakuri ban iya tashi na dora girki ba,Ina ta kwance.."

Murmushi Mama Safiya tayi a ranta tana sake jinjina irin karfin sa'ar da Hashim yayi na samun Abidan Amma ya kasa gani.

Tana tunani ta Kalli Abidan,da yarinya jajur da ita Amman yanzu bakin halin miji da muguwar rowar jaraba ta sa duk ta kwanzame kamar ba ita ba ,duk ta chanja .

Cewa tayi "kar ki damu Maman Abul,ba komai ai abun ne se a hankali  yanzu kam"

Dan yake Abidan tayi yayin da suka ji sallamar su Abul.ai suna shigowa suka ma Mama Saffiyya se murna domin Yan uwan Uban su ba karamin son su suke ba.kawai tsabar rowar ubansu ya Sanya kowa ya janye masa.

Zaka ruga rabar Wanda yake ganin kamar kullum arzikin shi kazo ci ne ? Ai baze yiyu ba dan se raini ya shiga tsakani.

A dan haka kowa ya ja jiki ya zuba wa sarautar Allah ido.Kuma suke zaune lafiya ba tare da kowa ya damu da shi ba.

Gaishe ta suka shiga yi suna tambayar ta ya gida ,akwai yaron ta me suna Auwal sun Saba da Abul duk da shi yayi 17 ma dake Yara biyu gare ta .ta farkon mace ce me suna Fatima Amman tana Aure a Zaria .ita ma ta haihu .so se Auwal din kawai ne a gaban ta yana jami'ar KUT a shekarar farko da yake ya samu shiga ba tare da wata tangarda ba

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now