Sauyin rayuwa (2)

127 7 0
                                    

SAUYIN RAYUWA (BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

MONDAY,28TH FEBRUARY,2022.

(2)

__________

A yayin da take tsaka da tunanin ta,dole ta tsaya chak,Dan duk gigin tunanin ta Bata Isa ta bar yar shinkafar nan tasu ba ta Kone,yo in ta Kone wa tawa? Kansu.

Dole ta yunkura ta tashi ta duba shinkafar wadda ta dahu ligif dai dai da bukatar ta.

Sauke wa tayi ta kwashe a wata kula,kwanon mai ta Maida wuta ,ba maganar albasa ta dumama musu shi Shima ta sauke ,tana cikin kashe wutar taji ana taba gate ,tasan yayan Albarka ne suka dawo.

Da yalwar fara'ah a fuskar ta ta nufi gate din ta Bude wa farin cikin zuciyar ta,kan ta karasa ma ta ga Nabila karamar ciki me shekaru hudu ta shigo.Nabila uwar kankanba da iyayi suna mata lakabi da likita . ta shigo rai a bace .

Bayan ta Saudat ce me shekaru 8 uwar tsokana kenan ga barkwanci ga rashin hakuri da son girma ga kaunar Yan uwan ta.wannan professor kenan Dan akwai ta da son karatu ga jarabar tambaya,komi ta ga Bata sani ba se ta tanbaya haka take ko a aji.

Se Zahra wato Zareriyar maman ta me shekaru 12,wannan langwai kenan uwar miskilanci ga sanyin jaraba kamar kankara,ga son Isa kamar wata sarauniya.ita kam Zahra Daman lakabin ta matar sarki ne.

Se Babban Yaya Abul-khair me shekaru 15,wannan uban Alheri kenan.a yadda basu da shi,suke fama da Rashi,Suma basu wadata ba a haka yake bayar wa matukar yaga me bukata,ga kirki gashi da son maman shi kamar ya cinye ta danya.Abul kenan, shi kuma lakabin sa Barrister ne .

Da fara'ah Maman Abul ta tarbi Nabila tace "Ah ah waya taba mun Dr haka a wannan ranar.."

Shiru nabila tayi ta Wani gyara tsayuwa ,Maman Abul ta Kalli sauran Yaran dake tsaye suna kumshe dariyar su.

Rungumo Nabila tayi tana juya wa tace "Zo likitar Maman ta,muje ki gaya mun Wanda ya tabaki,a wayo fa ita ma Maman Abul din dariya take boye wa,Dan tasan halin Nabila,Drama queen ce akwai iyayi.

A tabarmar dake shimfide daga jikin garun tsakar gidan babban gidan nasu suka yada zango .

Kafafun Nabila Mama ta kama tana cire mata designer takalmin da tsaraba Adda muhsina ta kawo musu,tana cire mata cikin murya me taushi tace ..

"Dr waya taba min ke,autar Mama guda waya Bata mata rai?" Ta Maida akalar tambayar ga sauran Yan uwan

Zahra dai murmushi tayi tana linke dan hijabin da ta cire.daki ta wuce tana tafiyar ta cikin sanyin jiki.

Saudatu proff ce tace "Mama wasu ne kawai suka tsokane ta ,wai Nabila yar sukuta ".dake Nabilan irin dirarrun Yaran nan ne masu mulmulallen jiki,Kai kace irin goyon Horlicks da su rice krispies ne.nan ko Iko ne na Allah kurum dan Nabila duk Bata ma San wannan Abubuwan ba.

Maman tasu dai ita Allah ya mata lidifi ta sani .

Kallon Nabila tayi da alamun ranta ya baci dinnan "tace su waye,ke Baki San burge wa kike da lutin jikin nan naki ba,Suma fa na gane so suke su zama irinki shi yasa suke tsokanar ki.

Haba me saudatu zatai ba dariya ba.

Maman ma dariyar take kokarin yi musamman yadda Nabilan ta turbine fuska .ga tsokar fuskar tata tayi kitir-kitir uwa irin sabon kindirmon nan.

Abul da ya ke dakin ma Dariya yake yi,Dan yana kallon su tunda a Bude yabar kofar dakin nashi.

Zahra ma murmushi tayi dake ta fito tsakar gidan tana dan karasa ayyukan da Maman Bata karasa ba kan suci abinci.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now