SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(50)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Barkan mu fa shiga sabuwar shekara.Allah ubangiji ya hada mu da dukkan alkhairan da suke a cikin ta,sharri Kuma ya kare mu daga su.Ameen
Bayan shigar queen gida ta gaida mama ta shige daki ta samu gu ta zauna tana tunanin karfin Hali irin na Dr.
In banda ma shi,ya za'ai yace wai ta gaya wa ,ko shi ze gaya wa mama zasu je gun aiki tare ?
Ai in shi be sani ba,ita ta san ko a wasa mama baza ta yarda da wannan tsarin ba.
Hakan ne ma yasa ta samu gu ta kwanta tana tunanin abun yi
A ranta take tunanin Kila ma ya tafi dan yaga shiru bata koma ba..
Cikin wannan tunanin take tsinko muryar Nabila ta yo sallama tana cewa "mama wai inji Yaya yace wai Adda Zarah taje lokacin na kurewa"
Kan ta motsa taji Maman su ta doka Wani salati tare da ambaton sunan Zarahn..
Fitowa tayi tana zare idanu Jin me maman tace ..
Cewa tayi"yanzu ke dan wauta kin San ana jiranki a waje shine kika shige dakin kika kwanta dan rashin hankali?"
Tsugunnawa Zarah tayi kafin tace "ah ah mama,na zata fa ya tafi"
"Ya tafi,ya tafi Kuma? Maman ta maimaita kafin tace "toh da ke baki san ko ya tafi ba ko be tafi ba ne kika shigo ko ko da ya aka soma?"
Kyafta ido Zarah tayi kan tace "Mama fa cewa yayai in zo na gayo Miki zan raka shi gun aiki,ni Kuma bazan je ba ne ya sa nake jiran Nabila tazo na aika ya tace kince ah ah"
Wani salatin maman su tayi tana cewa "ni nake jikar mutum hudu,karya ko kike mun Zarah,wai shin ni ke Kuma girma da karya yazo miki? Mene wai ribar karya a rayuwar duniya ne,shin Ina laifi a fadar gaskiya ko da in kin fada za'a tsire ki? Haba fadima ,ya abun da bakiyi ba da kike neman fara shi yanzu?,da wayon ki fa komi?"
Tuni Zahra ta fara hawaye kafin tace "toh Mama ni bana son abubuwan da yake mun shiyasa nace bazanje ba"
Baki bude mama zaune a tabarma tace "oh .Allah ba gode maka,ni ban san amfanin wannan abun naku ba wallahi,Allah ya kyauta.ince dai ba yanka ki yake ba ko?"
Zarah ta daga Kai,se maman tace "ai da sauki ,yanzu tashi kije ki raka shi aikin,in kin dawo zamuyi magana"
Baki bude Zarah take kallon mama da tunanin ko maman bata ji me ta fada ba ne.
Cewa tayi "Mama fa tat.."
Katse maganar da Zarah ke kokarin sake yi maman tayi tana cewa "Zarah'u tashi ki wuce jar in tsin-tsinka Miki Mari"
Sumuy sumuy Zarahn ta tashi daga tsugunnen da take ta juya ta wuce daki.
Hijab din ta ta Sanya ta fito ta fice daga gidan, dan maman na gama mata magana ta dau buta ta fada bandaki ba tare da bukatar yin komi ba a ciki ..
Dafe da Kai take mamakin halin ya'yan zamani..
Aiko Indai haka ne gwamma a tattara a harhada me za'a harhada a Mika masa ita chan suje su karata ..
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Ficción Generallabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...