(30)

49 8 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(30)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Baki sake maman su take kallon Zahra da ta shigo ciki da gudu ta wuce daki ..

Cikin dakin Maman su ta bita tana tambayar dalilin gudun nata..

Zahra ce tace "shine wai se nace ummm ,nikuma na gudo mama,ya sa ma na zubar da kayan kwalliya ta again"

Sakatotoo maman tayi tana kallon Zahra.

A ranta Kuma take cewa   "a haka za'ai auren?"

Maman ma bata ce komi ba saboda kunyar abun gaba daya da ya kamata,se tace da Nabila dake tsakar gidan ta samu taje waje ta kwaso kayan da Zarahn tace ta zubar.

Da ta fita ta tarar da Sufyan yana waje yana Jira,kamar dama yasan dole se wani ya fito kwashe kayan.

Cewa tayi "Laa baba kana nan?"

Yace "eh kanwata ,Ina nan ,Ina Addar take ?"

Cewa tayi "Tana cikin daki ta buya "

Dariya yayi sannan yace "Me sunan ki ke?"

Tace "Dr Sunana.Dr Nabila"

Yace "Lalala kice kema Dr ce,Nima Kuma Kinga Dr ne fa"

Cike da kauna da mamaki ta bude baki tana murna sosai ,Dan Nabila tana son Dr's har ranta,saboda Dr ma take son ta zama a rayuwar ta in ta girma..

Cewa yayi "Toh Dr Nabila,kije ki amso mun number din wayar Yayar ki ga wayata "

Ya fada tare da miko wayar  yana cewa ,wannan Kuma a Kai mata..ledar kayan da suka zube ce

Shiru ta danyi kafin tace toh,amman inna amshi wayar Mama zata iya yin fada,se dai naje na gayo mata ,amman fa addan mu bata da waya,se wayar Mama kawai. se ta amshi ledar tace zanje na dawo .."

Shige wa gidan tayi,tawa mama bayanin wai yace a bashi number Adda zahra,gashi Addar ba waya ba gare ta ..

Tunani Mama take yi na yadda za'ai tunda dai Zahra babu wayar ma balle wata number waya ..

Cewa tayi "Amshi nan ,ki Kai masa ya Sanya number din a nan.."

Mama zata tsaya wasa ne,ga dama ta samu? ? Tuni ta mika wa Nabila wayar ta Kai Mai.

Zuwa Nabila tayi ta Kai Wa Sufyan wayar Mama tace "wai mama tace ka sanya mata number a nan,ita bata da waya"

Amsa yayi ya rubuta number din sa a wayar ya Mika wa Nabila.

Amsa tayi ta ce "Angode se anjima "

Har zata shige se ya tuno cewa ,Kila Zahran zata iya kin Kiran shi ko da an Kai mata number din,which is fair tunda dai mace ce Kuma ya lura akwai ta da kunya ..

Kiran ta yayi ya sake amsar wayar se yayi dialing number din ta shi dan yaga tasu number din..

Kiran farko aka shaida mishi cewa babu kati a cikin wayar..

Amman an samu beep call ya shiga so ya samu ya ga number din.

Saving ya fara yi da "maman Zahra"

Sannan ya musu recharging da 5000 naira ,ya mika mata yace ki Kai Wa Maman kinji Dr,sannan kice wa Adda zan kira ta wuraren 7 ta zama wayar na hannun ta.."

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now