SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(16)
_______________
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨A hanyan ne ma ta rasa yadda za tayi,se a lokacin ma ta fara tunanin shin Ina ma zata je.
Kawai se ta dauki hanyan court road,Kuma bata tsaya ko Ina ba se court.
Ta yi parking motar ta ta sauko ,Asif ta Goya ta dauki Arif a hannu ta nufi cikin inda take zargin nan ne zata iya tambaya akan abun da ya kawo ta.
(Yauwa ni ban taba zuwa kotu ba bare nasan yadda ake Wani bin tsari,sannan nama yi ta kokarin kotun zan aika Abida se court din nan na iya tunawa ,saboda haka zan rattaba muku abunda naga dama tunda nidai ba hadisi nake rubutawa ba bare ace na kauce fadin gaskiya na zura tawa karyar .Yauwa zan fadi abunda nake zaton ze isar da sakon da nake son isarwa fakat!.Awo inji sakwatawa )
Wani mutum ta samu Wanda yake taho wa hanyar fita da alamun ma fita ze yi .gaishe shi tayi sannan tace
"Baba dan Allah Kara na kawo"
Cewa yayi "toh"
Dan juya wa yayi yace "biyo ni muje naji karar wa kika kawo"
A tare suka juya ta bishi suka shiga Wani office .
Ashe ma judge ne bata sani ba .
"Ina jinki " yace mata
Dan shiru tayi tana tunanin me zata ce .chan Kuma se tace.."Baba Aure na nake so a raba mun.."
Ta karasa tana Dan kallon yanda ze dauki maganar tata.Kallon ta yayi a tsanaki yana so ya tantance abunda tace ,ba wai dan be Saba da ganin haka ba,ah ah kawai dai yadda ya ganta responsible ne yasa yaga kamar ba za tayi hakan ba..
Yayin da hawaye ke gangarowa abida yana diga kan hijab din ta gwanin kashe zuciya.
Yan biyu sun yi bacci dama ta goya daya,dayan kuma na sakale a kafadar ta tana dan shafa bayan shi a hankali.
Da yaga bata tsananta kukan ba se yace "ko mene dalilin ki da yasa har kike so a raba auren ki,kinsan fa raba Aure ba abu bane na wasa,sannan bama raba aure har sai in da ya kasance akwai kwakwaran dalilin da ze sa a raba shi.ko kin San cewa Allah da Ya Hallata saki ma baya son shi?"
Da yake tambaya ya mata se ta daga Kai.
Se yace "toh me yasa kike so ki kashe naki auren?"
Alkali Ibrahim Ibrahim kenan.Alkalin da yayi shura sannan yayi suna a kan makamin sanin aikin sa,alkalin da akayi masa tambarin Shari'ar gaskiya.
Alkaline shi Wanda tun da ya fara yanke hukunci be taba yanke na rashin gaskiya ba,domin baya taba yanke hukunci ba tare da dogon bincike ba.
Ina irin a zartar da hukunci din nan ba tare da an tsaya an gano gaskiyar me gaskiya da karyar me karya ba,ko Kuma Kiri Kiri shari'a Taki gaba saboda anayi tsakanin me karfi da mara karfi? Toh Alkali Ibrahim be taba wannan ba har kawo yau.
Da kanshi yayi hiring private investigators,Wanda ko irin shari'a ake in an fito Hutu akan ga masu Kara ko Wanda akayi karar sa sun ja gefe suna maida yadda aka yi? Yawwa toh da Mutanen shi da me tsaya wa a gefe ake wannan tattaunawar.
Masu gaskiya suna takaicin yadda masu karya ke hakikan ce wa akan karya.
Yayin da masu karya ke ja gefe su ruga fadar laifin su da kansu ba tare da sun San cewa akwai masu Jin su ba.
![](https://img.wattpad.com/cover/291299833-288-k449880.jpg)
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...