SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(60)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Ko da queen ta farfado taki magana ,ko kukan ma kasa Yi tayi,se kawai ta runga bin su a hankali da Ido ...
A farko ta manta me ma ya faru ne ,se daga baya ta tuno,Shima da tuno din kasa kukan dai tayi,haka sukai ta bata baki da nuna mata mama tsokanar ta kawai take yi sannan fa ta dan Yi normal..
Bayan doguwar nasiha ya dauke ta suka tafi suka shiga gidan su..
A wannan gida queen taga gata taga tarairaya,se nan nan ake da ita..
Shi kuwa sarki ya kafa ya tsare ,a dole matar shi bata da lafiya ..
A nan ma sun musu nasiha me ratsa jiki shida ita ,Alhajin su ne ma baya nan,ya tafi Abuja,so haka suka tafi a washegarin ranar Kuma suka kama hanyar kuzoma da tambura,da algaitu na wayanda suka taho tafiya dashi,ga algaitu na Isa da Iko da alfarma se tashi suke..
Haka aka tafi da Zahra a dogon convoy, abubuwan suna ta bata mamaki ,wai yau ita ce matar Sarki,har gashi suna tafiya a convoy..
Bata Kara tsinke wa da lamuran ba,se da taga an tsaya a hanya ,wasu motocin hakimai sun tare su,anyi wa sarki gaisuwa sannan an sake daukar hanya aka tafi kuzoma a kasaice ...
Lallai sauyin rayuwa ba yadda baya zuwa wa dan Adam..
A bangaren ta aka sauke ta Shima sarkin a bangaren shi,amman yace shi matar shi baya so tayi nisa da shi gaskiya,ba maganar wai Dan shi sarki ne a raba sa da matar sa,yafi son ta a kusa dashi tunda ya San dadin kayar sa,haka ta dawo bangaren shi suka fara zaman su kamar dai yadda suke a gidan su..
A wannan gari na kuzoma queen Taga gata da sangarta . ...
Wai tafiya ma in tana Yi ana ce mata "takawar ki lafiya,a takaice ma kamar su mata tafiyar haka suke mata..basa barin ta yin tsinke komai mabyi mata ake yi
Gashi bata aikin fari ko na baki,ga fadawa ga zagagen sarki ga jakadai,haka ita ma duk tana dasu ..
Toh Alhamdulillah..
✨💞✨💞
Sun samu wata daya a kuzoma ,kullun suke Kiran mama suyi ta addabar ta,wani bin musu suke Yi ta raba musu,wani lokaci Kuma fada ne suke a wayar, haka mama take ta fama dasu kullum ne se anyi haka ...
Kamar kullum din yanzu ma sun gama musu ne akan se mama ta fada musu Wanda tafi so, Sufyanu yace mama tafi son shi,queen tace mama tafi son ta,shine aka kira mama ta raba wannan musun,ita kuwa tace "Kai ni bana son ku duka se kunyi hankali" nan fa sukai ta dariya kafin ya anshi wayar Yana shawara da maman akan asibitin da yake so ya gina me kyau a masarautar..
Kusan dukkan shawara na masarautar da ita yake yi,ko be kira iyayen sa ba to ze kira maman matar sa..
Bayan sun gama shawara ne yake cewa "Mama ku shirya anjima Bashir zezo ya fita daku se a siyo abubuwan amfanin ko,gobe in shaa Allah se azo a kwaso su.."
Mama Cha take "toh in Sha Allah,za'a taho da Nabilan ne? Yace "Eh shiyasa zasu taho da Jakadiya Tabawa ,babba ce Kuma an mata shaidar Amana"
Maman tace "tohm in shaa Allah,Allah ya kaimu goben"

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Fiction généralelabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...