(61) haduwar masoya

70 6 2
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(61)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Ita ma a bangaren ta zuciyar ta fal soyayyar Abid din ta a zuciyar ta..

Se dai yadda tayi gaba daya se ya tsorata shi.. meaning ta hade girar sama da ta kasa

Kayan motsa baki ta hado masa sannan ta zauna a kasa tana kallon carpet..

"Baka tsoron me gidan ya dawo ya ganka ?"

Cewar Abida bayan ta zauna

A  dan razane ya dago kan shi ya kalle ta,se Kuma yace..

"Shiyasa se yau nazo ai"

Kallon shi tayi a hankali sannan ta sake cewa "baka dai tsoron kenan"

Daga Kai yayi..

Bece komai ba se kallo da Ido..

Kallon shi tayi yayin da yayi mata wani irin Abu da idanun ta,se tace "basa nan duk,sunyi tafiya "

Yadda akai ta gane me yake nufi se ya daure mai Kai..

Ganin cewa yasan sun rayu tsawon watanni 7 da Aishatu,amman har yanzu bata gane maganar shi da ido..

Shiyasa duk sanda ya kasa magana se dai tayi ta al'amuran ta ita kadai,ma'ana in tazo yi mai magana,se dai tayi ta chanki chanka..

Amman da ya tuno tun asalin sanda ma Abidan take da kuruciyar ta suke magana da Ido se yaji sanyi a ransa ...

Kallon ta ya sake Yi,da alamun wata tambayar,se tace..

"Aure,aure na ya mutu ,Kuma a sanadiyar ka"

Wani irin mayataccen kallo ya zuba mata Jin abunda tace .  ...

Gaban sa hatta faduwa da tashi yanayi ..

Alamun ban hakuri yayi mata da idanuwan sa da kwalla suka silalo..

kallon wayar sa da take gefen kujera yayi se ya dauka ya mika mata..

Kallon shi tayi kafin ta rubuta masa number din wayar ta,abun kamar a a mafarki,wai yau ita ce gata ga Abid,se kace a shekarun baya ..

Mika masa wayar tayi saye da murmushi a fuskar ta..

Kallon ta yayi kana Kuma ya sumbaci wayar,sumba wadda ta dauki lokaci ,sumba wadda take tafe da wasu irin rikitattun sakonni,sumba wadda ta bayyana mata al'amura masu wuyar sha'ani,sumbar da ta Sanya taso ta manta kanta,sumbar da take dauke da ban hakuri,roko da nadama duk a ciki,a kalla sumba ce wacce ta dauki kamar mintuna uku duk da a jikin wayar da hannun ta ta taba yayi ba ga itan ba..

Hooo wallahi soyayya gaskiya ce ,Ni dai a nawa tsarin Ina jinjinawa Kuma sannan Ina daukaka al'amari irin na soyayya..

Tuni hawaye ya fara zubo mata a fuskar ta,kunya da kawaici da kaara da nadama da da na sani da komai  ma se ya rufe ta ...

Jiba Kuga irin masoyin da ta bari ta auri Wanda be taba mata soyayyar gaskiya ba,Wanda yabi dalilai wajen raba ta da farin cikin rayuwar ta ..

Tabbas tayi rauni tana cikin wani mawuyacin hali..

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now