SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(44)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨💞✨💞✨💞✨
Toh mutane na,ba abunda kuke zato bane ba atoh 😂
✨💞✨💞
Mika yayi na gajiya,ita Kuma ta wuce saboda ta gefen shi saboda ya kulle kofar motar ..
"Muje" ya sake fada bayan kulle kofar..
Gaba sukai kadan zuwa kofar shiga gidan,ita Zarah ta tsaya daga baya,shi kuwa yayi sallama
Mama da take zaman jiran dawowar su cike da damuwa da fargabar rashin sabo da sanin inda suka tafi ce ta amsa sallamar Sufyan din hade da cewa..
"Ah ah Bismillah" bayan ta ajje yar guntuwar ajiyar zuciyar ta na ganin sun dawo duk da ma tasan sun cewa sun fita din...
Kun tuna wayar da Sufyan din yayi dazu Yana cewa..
"Wa'alaikumussalaam duba message din ka" ? Toh ya aikawa Abulkhairi message din cewa ya gaya wa Mama dan Allah ze fita da Zarah ta dan sha iska na damuwar da take ciki da koke koken da take yi din nan ne..so tasan sun fita din..
Ciki ya shiga ya zauna a kan shimfidar tabarmar da ke gefen ta maman Yana cewa
"Mama 'yayan ki sun bace ko,ayi mana afuwa,zuwa mukai daga siyan kayan kwadayi Zarah ta dinga zura mana kuka kamar an dake ta"
Murmushi tayi na yadda kiri kiri Sufyan ya dage da wasa da ita,Kuma yaki jin kunyar ta, sabida ya mugun sakin jiki da ita ne fiye da kima ..
Kofar take kallo alamun neman Zahra ..
Ganin haka se yace .. "Taki shigowa ne,Dan tsoro take kar musha duka,niko nayi wayo nazo na fara bada hakuri kar laifin yayi ta tsawaita,yanzu Kinga ita kawai za'a daka ko mama?"
Murmushi tayi sosai dan Sufyan badai Saka raha ba,a zahirin gaskiya Kuma har da ciwon ta da yake so ya kar yayi mata mugun yawa ne ya sanya yake son saka ta farin ciki a ko da yaushe,da yake doctor ne,yasan me dame ya kamata yayin Wanda ze taimaka wa Karin lafiyar tata...
Cewa yayi "Uhm bari naje dai na gano me ya tsaida ta wajen"
✨
A kofar ya tadda Zarah a tsaye ta dafe kirjin ta cike da tsoro da tunanika cewa yayi
"Mama fa tayi bacci ma,zo muje ciki"
Kallon sa take cikin son tabbatar da gaskiyar maganar da yayin..ganin ba wasa a fuskar sa yasa ta gasgata maganar tashi.
A hankali ta fara taka wa har cikin gidan,tana shiga ta ga Maman a zaune, zuwa tayi ta fada jikin ta tana kuka tana bawa Maman tasu hakuri..
Dariya maman tayi tana cewa "Ho zarah ke kam kin kasa girma ,'daga nikam kafin ki karashe mun dan bayan nawa "
Sake kamkame maman Zarah tayi tana kara bata hakuri..
Saboda dariya ma maman kasa magana tayi,daman Kuma haka Zarah take mata in dai ta tabbatar tayi laifi..toh fa in ta kamkame Maman har se tace ta hakura sannan take cikata..
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...