SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(15)
_______________
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Bayan dogon kuka da Abida ta Sha a inda take tsugunne se ta samu ta lallashi kan ta ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya.
Ashe wannan bala'in na shekaru da yawa Abid ne ya ja mata,toh mene dalilin sa kenan in dai haka ne ?
Ai ta zata da yace ze yi respecting decision din ta as a man of his word ze cika.
Toh mene gain din shi a cikin yin Hakan?
Shekarun da yawa,but still she needs to find out why he did that.
Se dai kuma deep down a ran ta da irin sanin yakamatan da ta San Abid na dashi tana kyauta zaton cewa baze yi Wani abu dan ya cuce ta ba.
Se dai mutum Kuma dan adam ,kilan ya kasa ruke yadda ta zabi Wani akan shi ne yayi abunda yayin.
Amman fa duk da haka tasan ba tabbas ace da Wani nufi yayi dan ya lalata mata rayuwa.
Yo lalata mata rayuwa mana.
Ina ce se an samu jituwa da soyayya sannan ake Jin dadin zaman auren?
Toh Abida dai duk ba ko daya,don tsakani da Allah Abida Bata Wani San rayuwar Aure me dadi ba.
Naji duk tsanani akwai kwanakin dadi a cikin su,akwai sanda Hashim yake chanja wa daga yadda halayen shi suke.
Amman fa ba Wani chanjin azo a gani ba,misali ran da yake cikin nishadi ko ya samu alheri ta bangaren kasuwancin sa sosai se yayi ta faman murna.
Toh a irin ranakun ze iya Bada magi biyar ma ,ko ya Bata taliya uku ko Mai na girki me dan yawa ba irin dan tsirit din da ya Saba bada wa ba.
Kunga ai halin ya chanja daga ba kullum ko?
Toh Amman irin yadda Abida ke karanto rubutacciyar Kuma shiryayyiyar kauna a novel duk ba ta San su ba a zahiri.
Kai ita fa Abida har tantama take ko ita cikakkiyar mace ce,yo eh mana,ace Namiji ya Sanya kana tantamar ko cikakkiyar mace kake ko ba haka ba ai ya lalata maka rayuwa kenan.
Baku gane me nake nufi ba ko? Dama na sani.
Toh abunda nake nufi shine ,duk wata cikakkiyar mace da gyara aka Santa,na jiki ne ,ah ah fuska, gyaran gashi da dai duk Wani gyara da ya kam tada kwalmada.
Toh su wayannan gyare gyaren su ne Abida ba ta iya su ba.
toh ko ta iya ma Babu amfanin.
Sannan ba kudin yin su,Kuma ko ka yi Miji be ma sani ba ko Kuma ya damu ya sani balle ma aO batun ya yaba .
Dama shi Hashim be dan San "plays" ba .kawai Kai tsaye ayi a wuce gun.
Toh a Ina zeji santsin fata? Ko kamshin gashi ? Kunga ai babu
So se Abida ta Saba da haka,tun da Miji ya nuna maka amfanin ka haihuwa ce kawai ai se ayi tayi.
gyaran gashi kawai take iya yi Shima dan tana da yalwar gashin ne sannan Kuma asali bata da kazanta.
Kai wallahi Abida ta gode wa Allah C's ake mata na,da ba C's bane yadda Yaya ke fitowa duk yadda suke so da yanzu ta zama sisi kwandemm.
Kar fa ku manta inda muke!
Abida kamar za tayi magana se ta tashi kawai ta fito ,yanzu ba ta da bakin cewa komai kam.
Toh fa tunanin da take ta yi kenan har suka Iso crescent din.
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...