SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(54)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Gun Yaya khairu suka zo suka tadda shi yana bawa su queen da mama labarin yadda ya gano proff din..
Su kuwa suna ta sauraren sa cike da zumudi da farin ciki..
Bayan su proff sun zo se ya sake mika musu wayar ya nufi inda su Abdullah suke..
A nan ne ma yayi musu dan takaitaccen bayani akan fitar daya ke so zeyi yaje ya dawo..
✨💞
Cikin mall suka nufa bayan mina ta gaida Yaya khairu din ,har a lokacin proff na waya da su mama bakin ta yaki ya rufu..
Ba ita ba,hatta su maman ma bakin su har keyar su tsabar murna da luguden dadi..
💞
A cikin mall din kuwa ko da proff ta Isa se kawai ta nika wa uncle Baba wayar tana cewa "Baba ga waya su adda su gaida ka"..
Yana kallon fuskar wayar se da gaban sa ya wani buga sakamakon ganin fuskar da ko a jiya kwana yayi Yana mafarkin ta saboda tsabar shauki irin na soyayya..
Cikin Jin kunya ta kauda wayar daga fuskar ta ta bawa queen..
Queen ce ta fara gaida shi kan su Nabila suka gaida shi suma..
Ita dai Mama Abida se ta background din ta gaida shi ya amsa yake tambayar ta sauran Yara ..
Yace "kawai se ga 'ya'yan ki yayan su ya nemo Miki su ko"
Murmushin mama tayi tace "nagan su kuwa Baba"
"Alhamdulillah" yace ganin yadda matar shi ta kafe shi da ido, sannan itan ma maman su Abul, da kunya take amsa masa...
Nan aka ba mama wayar ta gaida maman su Amina sannan sauran Yaran ma suka gaisa da su kafin sukai sallama suka kashe wayar cike da farin cikin Ji da ganin juna...
Wani irin kulli ne me nauyin gaske da ya dade da tokare makoshin mama ya samu fada wa ji kake tummmm ya wuce ganin yarta cikin koshin lafiya..
Sannan Kuma Abul ya gaya mata karatu suke ba auren da akai musu ,Kai wannan al'amari yayi wa mama dadi matuka..
Tare da Abul da Saudatu da ta kankame shi taki cika hannun sa don kar ta neme shi ta rasa shi,suka rankaya se gidan da su proff inda suke.
Tabbas wannan Ahalin naji musu dadi,Hira kam an Sha ta ranar ba kama hannun yaro.. ,Dan a wannan rana Abul beko koma gida ba,a nan yake Sanar da Saudatu auren queen da tayi amman ba tare da yace amman itama Bata San tayi aure ba.
Dariya proff keyi tace "wai Adda ta me shiru shiru ce tayi saurayi harda aure?"
Dariya yayi yace "wato Saudatu kina nan da tsokanar ki ko,se na gaya mata toh"
Dariya tayi tace "abun ne da mamaki fa"
Se yace "toh kefa ,waye naki saurayin,ko Babu?"
Murmushi tayi tace "Haba Yaya saurayi ni? Uhm uhm Babu"
Dariya yayi yace "ki dai fadi gaskiya"
Cewa tayi "ni banda saurayi da gaske Yaya,ba yanzu ba ma kam,Kai fa Yaya,bakai auren ba ,wace to bae din ?"

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Ficción Generallabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...