SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(57)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Bayan gin gidan hatta finishing din gidan irin su wall work , paint komai na gidan ya tsaru...
Kar Azo kan maganar furniture,ya zuba irin mazajen English furniture dinnan,gida ya hadu ya hade se jiran isowar amarya kawai yake yi...
Gidan ya burge queen matuka,yayin da ya burge maman ta ma ,ta runga auno yarinyar ta a wannan hamshakin gidan..
Godiya ga Allah tayi,ta sake, bayan ta share kwallar ta ,ta fara kokarin counting uncountable blessings din ta Allah yayi mata ita da ya'yan ta..
Sufyan dai dariya yayi tayi wa mama da su Nabila da har kowa ya ruga ya zabi dakin shi..
Bayan ganin gida da murna da nishadi ya maida su gida..
💞✨💞✨
A bangaren Su Alhaji Naufal Amarya Aisha ta bawa mara da kunya tace zata zauna da mijinta duk da baya son ta..
Abu daya take so,Kuma ta nema daga gun shi..
Ko Kun San mene ne?
Bayan iyayen sun bawa Amarya da angonta guri,se tace Mai.."Ina wuni"
Cikin nadama da tausayin kan shi da yarinyar ya amsa mata da "Lafiya Lau Amarya,ya biki,se akayi biki ango na asibitin ko?"
Murmushin tayi tana cewa "wallahi kuwa,Amman ai sauki ya samu yanzu insha Allah.."
Murmushi yayi mata Wanda kana kallon shi zaka San cewa yake ne ..
Girgiza Kai tayi kafin tace "naji maganganun ku da Hajiya fa"
Kallon ta yayi, yayin da kwalla ta biyo mata Saman fuskar ta..
Cewa yayi "kiyi hakuri"
Se ta murmusa tana goge hawayen ta,se tace "ai nasan maganar tun ba yau ba,kawai ta yau ce ta dake ni,kilan ko Dan na zama ina karkashin iKon ka ne yasa naji ba dadi"..
Kallon ta yayi kafin ya kauda kan shi..
Se yace "kiyi hakuri"
"Ka Daina ban hakuri,Abu Daya nake nema daga gun ka,Dan Allah Dan Allah kar ka sauke hakkin aure na Dake kanka face se kaji digon so na a zuciyar ka"
Kallon ta yayi,se yace "Indai kinji maganganun mu da mahaifiya ta ai kinji inda tace na sauke dukkan hakkokin da rataya a wuyana ko?"
"Eh" tace
Sannan ta sake cewa"wannan tsakanin ni da Kai ne,nayi Hakan ne saboda naga ko da gaske bazaka taba so na ba,ko Kuma wata rana zaka iya Jin so na a cikin ranka,ta Hakan ne kawai zan gane matsayin zama na a gidan ka,duk da ni na amince zan aure ka a haka,Amman na gujewa zaman gidan mu ne da zunden da mutane ke yi a Kai na na cewa Ina da Namijin Aljani ,shiyasa na kasa aure bayan kannai na duk sunyi aure,se ni kadai ce ban yi ba, dalilin da yasa naga Gwamma na auri Wanda yake ciwo saboda soyayyar wata,akan na zauna da wannan damuwar a Rai na..."
Kallon ta yayi kafin yace "Shikenan Aminatu,yadda kike so.."
"Aishatu dai Baba"
Ta gyara masa tana murmushin yake..wato sunan ta ma ya manta kenan?

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...