(27)

56 5 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(27)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Bayan yan kwananki shiru.gamu Kuma Allah ya bamu iKon mun zo xamu dora a inda muka tsaya ..

Ina Barar Addu'oin ku mutan Arziki 😀.Nagode Allah ya karba.Ameen

_______________

❤️✨❤️✨❤️

Kofar haddaden sanyayyen dakin Mimi ta budo ta shigo  tace..

"Sudee kizo inji Baba. yace Kuma yanzu yanzun nan yake son ganin ki"

kamo hannun wadda ta kira da sudeen mimi tayi tana share mata hawayen ta .

Mike wa sudeen tayi cike da jiri da hajijiya kamar zata fadi.

A hankali suka fita daga dakin ko wannen su yana share hawaye.

Se dai kowa da irin hawayen da yake yi,sannan Kuma kowa da dalilin yin hawayen nasa.

Duk da dai gaskiya ita Sudee kuka ma take sosai na tausayin Kai da gajiya da rayuwa.

Ita Kuma Mimi kukan tausayin halin da sudeen ta tsinci kan ta a ciki take yi,ko ba komai tana gwada kwatanta yadda sudeen take ji game da rashin maman ta da Yan uwanta.

Bayan nan Kuma na rashin sanin takamaimai halin da su suke ciki Wanda duk shi yafi daga musu hankali gaba ki daya.

Duk da zaman da sudee take a gidan su mimi ba zama bane na takura ko tsangwama.

Zama ne take na yanci da Jin dadin rayuwa,se dai tawaya guda daya da take dashi Wanda shine rashin uwa mahaifiya tare da Yan uwan ta da suka hada jini daya, Wanda ta rasa sanin inda suke.kunga ko ba komai ai wannan babbar tawaya ce .

✨💞✨💞

Mimi budurwar yarinya ce da ta samu kulawar iyayen ta tare da gata ,ga ilimi da tarbiyya me inganci.

Sannan Kuma Wanda makerin budurci yayi wa kerin kure karyar me kallo.

Mimi budurwar yarinya da zata iya Kai akalla shekaru 16-17 yanzu bayan shekaru da yawa da muka dauka bamu ji su ba.

Aminatu Yan matan Baba kenan.

Se Saudatu (Sudee) a yanzu, wadda ita ma dai makerin na budurci be barta a baya ba .

Ya kerata yadda kuka san marsandi S + C class. Ta wanku ta gogu tayi tar tar da ita alaji,ga kyau ita ma wanda Shima be kadan ba Kuma beyi yawa ba.

Saboda kulawar da ake basu se ya zamana sun gogu da tsafta da iya gayu.

Ga uwa uba kwalliya ta kece raini dan gaskiya Maman Amina ta tsaya a kan su da kyau Kuma sun gogu da gayu da tarbiyya.

Ko da yake dama ita Saudatu da tarbiyyar ta suka ganta,kawai dai an Kara a kan na maman ta ne.

❤️✨❤️✨❤️✨

A kofar haddaden falon Baba sukai sallama suka shiga.

Zaune suka same shi yana kallon shi .

A Yan shekarun nan uku zuwa hudu ya sake tsufa tunda dama ba wai yaro bane ba.

A kasa suka zauna suna sake gaishe shi bayan gaisuwar asuba ta ka'ida da suke masa a kullum.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now