(41)

46 3 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(41)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Daga gefin gidan Alhaji Hashim kuwa..

Kwance na gan shi daga shi se yar shara a jikin sa da Wani dogon wandon shadda daga gefen tsakar gidan babban gidan nasu.

Kallo daya zaka mai ka gane cewa baya Jin dadin Wani abu,musamman jikin shi da ya nuna alamun ba sauki tattare dashi domin kallo daya za'a mai a iya gane cewa yana Jin bebodi wato bayada lafiya Kuma yana jin jiki..

Sakinatu kuwa gefe take tana karatun wani littafin Hausa na Aunty divaa me taken "kaddarar rayuwa" ,yayin da take ta basgar raken ta cike da nitsuwar zuciya da nishadin karatun da take yi tana ta babbaka dariyar mairo da hasi ..

Ko kadan baza kace wai ita wannan ta zaunen ba ta san cewa akwai Wani mara lafiya Kuma me neman taimako a tattare da ita a dai yadda ta nuna.

Dan shagalin ta kawai take sha,dariya take ta babbakawa se kace me sabon kamun hauka,dama Kuma alamun sanyi ya dan fara busa wa..

Yunkurin amai ya fara yi cike da kakari cikin firgici da tashin hankali, aman ma ya ki fitowa,Ina irin tsiyar da amai yake yi dinnan,in  be nicci fitowa ba,se ya tsaya a tsakiya shi be fito ba Kuma shi be koma ba,se kai ta Jin shi a makwogoro ya tsaya maka ya Sanya maka tashin zuciya? Toh irin abunda Alhaji Hashim ke ta fama dashi kenan a kwance,ga abun kam ba dadi.

Ita kuwa Sakinatu ko kallo be ishe ta ba ma.
tunda gashi itan da za ta kula da shi din ba ta damu da damuwar shi ba,dan kallo daya tayi masa ta kauda Kai tana cewa ..

" in fa ka kuskura kayi amai anan gurin wallahi ka ma kwana da sanin cewa se ka gyara shi,dan kasan wallahi ba baiwar ka bace ni,da girman Ka da komai ka wani saki baki kyaaa ka kwararo amai ka zata zan kwashe,toh wallahi ban kwashe wa..ah toh Dan ma kaji

Ta dauke Kai,yayin da ta cigaba da sha'anin ta tana karatu, ba maganar ta tambaye shi ma  ya jiki ko sannu,balle azo maganar taimaka mai ya tashi din dan kar yayi mata aman a kwance ..

Wani irin tashin hankali yake ciki ga rashin nitsuwar zuciya,ga ciwo ga tsantsar rashin kula daga wadda wai yake mata lakabi  tare da kallo a matsayin na matar shi.

Girgiza Kai yake yi cike da nadamar rayuwa da da na sani wadda ta kasance keya ce..

Tuno rayuwar baya yayi wadda duk sanda ya kwanta ciwo,Yana ciwon ne gefe guda Kuma yana Kuma ci wa Abida mutumci amman bata taba kasa basa kulawa ba..

A lokacin fa har akwai wata amai da gudawa da ya taba yi, bayan ya ci wani balangu mai masifar dadi yayi mai karo saboda yadda ya zauna ya tashi kan naman nan,shi kadai ya cinye abunsa dama,be samma  kowa ba,sanda ya tashi ciwon shi ma shi kadai yayi abun shi.

Domin wulakanci da wahalar wa Yana sane ya ruga kwarara amai a duk inda yaso ,ba wai Kuma dan baze iya tashin ba,kawai tsabar iskanci ne da rishan arziki..

Se gashi yau,ya kasa tashin ma na gaske, amman tsoron yin aman yake a kasa dan yasan cewa kadan daga aikin Sakinatu ta tattaka shi daga kwancen da yake in ya sake yayi aman,sannan kuma ta Sanya shi ya kwashe aman dole yana so ko baya so..

A dole yayi ta matsa aman cikin halin kunci da tausan Kai.

Kai rayuwar duniya abun tsoro ce,in yau Kai ne gobe kuwa ga wanin ka ne.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now