(19)

53 6 0
                                        

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(19)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Isar sa kotu ya yi bayanin kan shi da sammacin da aka kai mishi ya biyo sahu.

Se aka hada shi da Alkalin alkalai Ibrahim Ibrahim.

A office da suke zaune se da Alkali yafi minti goma yana kare wa Hashim kallo,

A yayin da ya fara tantamar maganganun da Abida tazo dasu a kanshi,se yaga kamar wannan mutumin is responsible,

kamar baze yi Hakan ba gaskiya don ko a fuska beyi kama da mutumin banza ba .

Se dai da yake ya aika an masa bincike akan Hashim din,Kuma an samu dan bayani duk da dai ba me yawa ba ne Kuma be Wani basa haske sosai ba.

Amman yanzu in ya fara zabgo Mai tambayoyi masu rikitar wa har se Hashim ya samu ya natsu ya fiddo gaskiyar da ke bakin sa..

Shi kuwa Hashim iya durar ruwa cikin shi ya dura .

Saboda irin kallon da alkali Ibrahim yake yi masa,Yama kasa fassarar irin kallon balle ya gane Wani abu ma daga ciki .

"Alhaji Hashim"
Alkali ya kira shi

"Na'am ranka ya dade"
Ya fada yana sunkui da Kai kamar Wani bakin munafiki,ko da yake ai banbancin sa da bakin munafikin ba yawa ne dashi ba.

"Kai dai ba yaro bane ,sannan nan gun kotu ce ba gun wasa ba,Matar ka malama Abida ita ta kawo karar ka nan wajen sannan take Neman saki daga gare ka ta kawo hujjoji da yawa Wanda su zasu Bada damar kotu ta sake ta ta bata yancin ta.

Toh amman saboda ita kotu a kullum tana adalci ne ga kowa  yasa aka kira ka aji ta bakin ka"

Mamakin Abida ne ya kashe shi matuka se yace "yallabai wannan ai matsala ce ta cikin gida Kuma zata gyaru komai zai dai daita insha Allah "

Kallon kofar sukai yayin da aka kwankwasa ,ya Bada izini a shigo se ga Abida ta shigo cikin sallama ta same su.

Baban Abul ta kalla ta gaishe shi a mutunce sannan Kuma ta gaida alkalin.

Wannan abun da Abida tayi ya sake Kara wa Alkali Ibrahim ganin girman ta da kimar ta .

Waje ta samu ta zauna kafin alkali yace .."Ina sauraron ka Malam Hashim,kace matsalar gida ce za'a iya gyara wa ?"

Satar kallon Abida Hashim yayi yaga ko motsi batayi ba,se ya samu kwarin gwiwa yace "eh ranka ya dade "

Kallon Abida alkali yayi yace "malama Abida ga malam Hashim nan yace matsalar ki ta cikin gida ce ,Kuma yace za'a gyara,shin ya kika gani?"

Gefe ta kalla sannan tace "Ah ah Baba,na hakura da gyaran"

Mamaki ya kama Abul .lallai yayi sake dan Zaki ya girma.

Abul ne yace "Abida wato kin raina ni ko Ina magana kina karyata ni"

Cewa tayi "kayi hakuri" sannan taja bakin ta tayi shiru.

Alkali yace "Zaki iya sake karanto Mai laifukan da kike tuhumar shi dasu kamar yadda kika gaya mun?"

Daga Kai tayi sannan yace "toh Bismillah"

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now