(14)

55 6 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(14)

_______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Please Ina bada hakuri kwana biyu ban zauna ba,shi Kuma rubutu na bukatar natsuwa shi yasa kuka ga mun yi missing two days..Amman I'll make up to you guys InshaAllah.ku dai,ku biyo ni muje ...

💞✨💞✨💞✨💞

A wannan tsakani Baban Abul kwana biyar yayi baya gari, shagali kuwa ba irin Wanda ba'a Sha ba a gidan nan saboda tsabar sake wa..

Har fa su wainar fulawa aka samu damar yi,Banda haka ma har kosai suke Siya na safe ko yamma su ci abunsu.sanda Baban Abul yake nan kuwa ba'a Isa ba ..

A ranar da ya dawo gidan ya koma kamar yadda yake tun asali ba maganar dogon wasa ko dariya matukar yana gida .in ko ba haka ba yanzu se ya zage yaro tas tun daga sama har kasa .Dan ma bashi da dabi'ar dukan yaro,Ina ga da tuni se dai Wani zancen Amman ba wannan ba.

Watakila fa da se dai Kuma gawar su,Amman tunda masifa ce chan yayi ta abunsa tunda dai Bata fito musu a jikin su..

Two weeks later ..

Yau ne ranar da Saudatu zata fara zuwa makaranta,to Maman ta ce zata je kaita .

Bayan duk sun shirya suka fada mota tare,cikin murna da farin ciki suka kama hanya saboda lokacin ma 7 tayi ,su Abul aka fara sauke wa Wanda Shima Ss3 ya shiga.

Yayin da sarauniya ke ss1,Saudatu Kuma Js1 se Nabila da ta shiga primary 2 ita ma.ko lissafin yayi ko beyi ba,oho.

A hanya su Abul suka sauka suka shige makaranta Saudatu na ta daga musu hannu.
Hanya suka kama tare da Yan biyu da proff da ke ta faman murna tana sake Dan karkade uniform dinta se kace Wanda kura ta hau Kai.

A gefe kuwa Maman su ce da take ta kokarin danne wulakancin da Baban Abul ya zabga mata da safe Wanda ya haddasa mata ciwon Kai ..

Ita dai ta San ko a hauka ba Wanda ya Isa yace mata yar wahala ce ,se dai a yanzu dai da take nan gidan,wannan kam ta yadda cewa yar wahala ce ..

Haba wannan Wani irin wulakanci ne ?

Wato abunda ya hada su da Baban Abul tun shekaran jiya ne da dare,da yake ya dawo da wuri ranar,ya kama ran Asabar sannan Kuma a wayewar gari yana da daurin Aure.

Wai Dan rainin wayo shine ya debo mata wankin Babbar riga da yar ciki da wando ta wanke masa.

Abida kuwa dama tun da Dade wa ta kudiri cewa ta Daina wa Baban Abul wanki saboda ita ba me wankin shi ba ce.

Ta wanke nata,tayi na yayan ta sannan Kuma tazo ta runga Mai nashi? Toh an ma ji tana Mai wanki ,Amman fa shi dry clean ma yake Kai nashi,su kuwa nasu a wasa,haka suke haduwa suna wanke wa tare ..

A tuno baya ma,bari na gaya muku asalin dalilin da yasa ta daina masa wankin.

Kamar irin haka se ya bata wankin kaya set biyu
Ta amsa ta wanke masa,se daga baya yazo yana wai ce mata ta bashi kudin da suke cikin farin kayan da ta wanke..

Nan ta masa bayanin cewa bata ga kudi na a aljihun,se dai wata yar guntuwar paper da ta tashi taje ta dauko ta Mika masa ,sannan tace "kayi hakuri wallahi mantawa nayi ban baka wannan papern ba."

Wani kallon banza yake aika mata,irin kallon kin ma maida ni shashasha din nan.

Nan ya ce "ni fa banzo dan muyi wasa ba,dan dama ni ba sa'an wasan ki bane ba ,ki shiga ki fiddo mun kudi na "

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now