(39)

45 3 0
                                        

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(39)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Kallon Abul mama tayi tana Sosa gefen wuyan ta.

Cewa yayi "mama misali ace rasuwa yayi shi din ,za'a ce ne dole se an dawo dashi duniya sannan za'a auri yayan sa ne,ko za'a ce dan baya da rai se aki auren yayan sa?

Kinga ai ba'a haka ko,toh yanzu ma dama mu kaddara ya rasun kawai,Dan in be rasu ba toh yana Ina ? Shine abun tambayar a nan,bayan nan ma,ni zan aurar da ita Kuma ba abunda ze faru se alkhairi mama insha Allah "

Kallon shi take yi cike da tunanika,Jin yayi shiru se tace ..

"Uhm uhm Abul..wannan duniyar fa ba yadda kake daukan ta take ba.

Habar ta ta kamo tana cewa.."hmm bari Kai dai"

Bana tunanin zasu yarda suzo neman aure gun ka gaskiya,Kuma ma wai gidan nan"

Ta fada tana bin dan mitsitsin gidan nasu da kallo..

Cewa ta sake yi "sannan maganar ace ubanku ya rasu be ma taso ba tunda kuwa da ran shi..

Cewa yayi "Haba mama,babban wa uba ne fa,Kuma ma mama naga Zahran ma duka duka ma nawa take, har yanzu fa bata yi 20 ba?

In baza su iya auren a haka ba mene ma abun damuwa,babu,Dan  wallahi ni na ma fi son naga kowa yayi karatu a gidan nan mama,ko ba komai in da karatun ka rayuwa baza ta tagayyara ka ba,se kiga inda karatun ko Yaya Allah ze Sanya masa Albarka mutum ya amfani kanshi da Al'ummar Annabi Muhammad SAW.

Yanzu in sun shirya zuwa ace suzo nan mama, abunda yake nan dai shi zasu gani,ba Wanda be nan ba ko? ,in ya musu toh,in be musu ba ba se a  hakura da auren ba,dan insha Allah zan tsaya wajen ganin ke da kanne na kun samu ingantacciyar rayuwa insha Allah..

kuma ko fasa neman auren Zahra su kayi mama ai ba shi bane karshen rayuwa,Kuma zama a iya cewa ba rabon shi bace,tunda wallahi matar Wani bata taba auren mijin Wani ko ba haka ba mama?"

Ajiyar zuciya ta sauke tana dan girgiza Kai alamun yarda da maganganun shi cike da tunanin dai hade da kokarin yi masu fashin baki.

Yace "yawwa mama,toh yanzu mama dan Allah ki kwantar da hankalin ki,bama bukatar ganin ki cikin damuwa duk kankantar ta,Dan bazan iya jure abunda damuwar ka iya jawowa ba mama.

Sannan Kuma ni da kaina zan wa Oga Sufyan magana naji mene Shirin shi,sannan na gaya mai nine me bada auren ta,se Muji me zece ko maman mu?"

Daga Kai tayi kawai alamun amsawa,amma a zuciyar ta Kuma cewa take "lallai yaro yaro ne,taya za'ai wai azo neman auren Zahra,ba ubanta ba dangin Ubanta,sannan abun ya yiyu?

Kuma yaushe aka taba cewa Wani ya rasu bayan Yana nan a cikin wannan duniyar da ran shi daramdakai??"

Cewa tayi "Ni Abulkhairi,na zata mun gama magana akan irin kiyayyar da kake ta nuna wa akan Baban ku,duk lalacewar shi fa shine dai ubanku.kai kasan ba'a taba chanja wa tuwo suna ko?"

Yace "eh"

Tace "toh me yasa a kullum Kai baka so kaji an ambaci sunan shi,se ranka ya baci kabruga kokarin kawo wasu maganganun a Kansa?ince dai abun da yayin ya wuce? Ina ranar riko Abul,ace ka rike ubanka a ranka shekara da shekaru Abul,ka tsane shi,ka kasa barin abunda ya faru ya wuce?

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now