(34)

52 5 0
                                        

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(34)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Wani bala'in burge sa take yi a duk kallo daya da zeyi mata. Yama rasa yadda zeyi da ran shi saboda tsabar soyayya ..

haka yayi wa Mama sallama ya fita Asif da Arif suna ruke da hannun shi.

A mota ya dauko musu tobleron milk da chocolate ya basu kowa daya suka dawo cikin gidan suna murna,gaba dayan su suka ci,se Zahra ce bata ci ba,dan ko kallon inda chocolate din take ma batayi ba.

Se fa da mama ta matsa mata sannan ta amshi kadan ta Sanya a bakin ta,Wani gardin dadi ya narke ya fati tare da soyayyar Sufyan ya I ko wacce gaba dake cikin jikin ta..

Zama sukai suka ci kosai suka Sha Kokon su cikin natsuwa da Santi gaye.

mama dadi duk ya cika ta, tana Addu'ar Allah ya sa alheri a cikin wannan tarayyar tasu gaba daya da Sufyan.

Bari na takaice muku,da daddare ma a gidan Sufyan yaci tuwon dare suka Sha hira a tsakar dan karamin gidan su.

Tun mama na Jin kunya har ya nuna shi baya surukanta da ita,a mama ya ke kallon ta,ni Kuma nace "ko a Yaya ba",dole ta daina nokewan nan da take yi wai ita me suruki ta saki jikin ta da shi..

Dama Kuma ba wasu mugayen shekaru ta bashi ba,kusan befi shekara uku zuwa hudu ba fa ta bashi,shi Amman be sani ba kallon wata Babba yake mata..

Ni wallahi dama Maman yace yana so ba queen ba da abun se ya fi tafiya dai dai..😂

Amman tunda yar yace yake so bakomai ai duk daya .

Tun daga ranar kullum se yaje gidan daga gun aiki.achan ma yake cin abincin dare abun sa.

Kuma ko a wasa be taba tsaya wa a waje ba yace Zahran ta fito,cikin gidan suke zama suke hirar su..

Gashi tarbiyya da hadin kan yan gidan ya dada shi da kasa matuka,sannan ga soyyayyar dake tsakanin su da junan su ita ma abun kallo.

wata iriyar soyayya yake wa ahalin gidan gaba dayan su,tun daga kan uwar har yayan ta.

Ya maida gidan gun zuwan shi ,wata rana in yazo Zahra ta kula shi,wata rana Kuma tayi gum kamar kurma in yan miskilancin nata suka motsa ..

Hakan be taba damun shi ba,zasuyi Hira dasu Asif ya tashi ya tafi.indai yana ganin ta ai komai normal ne.

Ya kan siyo musu biscuits da sweets haka ya kawo musu in ze zo,da Yake me ciye ciye ne.

Ko su rake,gyada da dai sauran su be cika zuwa hannu rabbana ba..

💕✨💕✨

A yau sun samu sati uku da fara tsaftataciyar alaqar su wadda kowa yake Jin dadin ta daga nasu bangaren, se shi Sufyan din da Abul kowa murna yake da alaqar..

Kuma be sake basu kudi ba tun wanchan lokacin.

Abu na farko da ya fara fuskanta shine ,daga sanda ya basu kudi ya lura suna yin abinci a wadace,ga girkin su Dadi ba kamar su nasu abincin gidan da Yan aiki ke yi ba.

Sannu a hankali,se ya lura da an samu chanji daga yanayin dadin abincin,ko wadatar kayan Hadi da dai sauran su.

Se ya lura kamar kudin nasu ne ya kare,shi da a ya  kwanakin ya kula da cewa shi kadai ake sawa nama a abinci har yanka uku ko hudu Wani lokacin.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now