(24)

56 7 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(24)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

✨💕✨💕✨

Wallahi na rasa yadda kike tunani soffy,ke ko tausayin su Mum bakya ji?

na baki hakuri na baki hakuri kinji kiji,na Baki shawara kinki ki dauka.

nima na gaji,na gaji wallahi,zan fita harkar ki kiyi tayin yadda kike so kiyi.

Kuma wallahi zanje in gaya wa su Mum ince lafiyar idon ki Lau duk iskanci ne saboda wani alkawarin ki na banza da kika daukar wa kanki.

Zan gaya musu cewa Saboda Namiji kika nakastar da kanki ba dan komai ba dan kar ki samu me auren ki.

wallahi in kikayi wasa tun daga farko har zuwa nan zan fetse musu su San komai,sannan koma miye ze faru se dai ya faru .wannan wallahi tsantsar rashin adalci ne ,munyi tare Amma yanzu zan zare hannuna.

Cikin kuka take karasa maganar ta saboda tsabar haushin soffy da Humaira take ji.

Hummy kenan .kawar soffy tun suna crescent.har suka gama basu rabu ba.ko su jamb ne post UTME ne duk tare sukai Kuma Allah ya taimaka suka ci.

Bayan an koma school a wanchan lokacin soffy bata nan.

Ina nufin sanda zata fara neman sistern Abul , lokacin ita soffy aje Lagos gun sister din ta dake Aure a chan Lagos din Hutu..

Bayan taje ta danyi hutun kadan se ta damu zata taho,amman sistern ta  taki barta ta dawo..

Ga Lagos ba nan ba.sanda ta tashi dawowa har anci term guda .

Kwatsam se Dad dinsu ya fara rashin lafiya,da mum da dad suka tattara suka tafi waje,Hakan ne yasa soffy ta fasa dawowa tunda dai ba Wanda zata zauna dashi a gidan.

Abunnan ya bawa soffy haushi matuka gaya.amman ya zatayi?

Haka ta hakura ta zaune.ko da yake ma ko bata hakura ba ma tayi a banza,su dad suka shantake a UK kamar baza su dawo ba .

dama da yake akwai Brothern soffy a reading.ko da zata je karatu a chan zata zauna a reading din tayi university din chan.se ma ta fasa zuwa.

se suke zaune a gun shi dad na zuwa ganin Dr.gefe guda suna hutawa da mum abunsu.

Bayan ya warke ma suka ci gaba da zaman su coz like suna da permission na zama a UK din ko zuwa yaushe ne ma.

Dole aka sake cin wani term din Soffy naji tana gani kamar zatayi hauka..

Sanda ta gama yanke shawarar zata gudo daga Lagos din kome ze faru ya faru,se kwatsam results din su ya fito sannan Kuma ana maganar su Jamb din.

Dole aka tattaro soffy da Aunty fatima sistern ta suka zo Kano.

A wannan lokacin soffy taje school din tana Neman su zahra dan an koma hutun third term.

Koda ta tambaya aka ce mata sun daina zuwa .gashi su Saudatu ma sunje Hutu daga gidan uncle Baba,se a week din ma zasu dawo so se soffy tayi tunanin ko maybe an cire su ne gaba daya ..

A ranar kam soffy Tasha kuka kamar ranta ze bar gangar jikin ta..

Haka ta hadiye murnar ta ta koma ciki.sannan ta koma gida dan Hummy ma a time din tayi tafiya.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now