SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(62)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Yayi saurin shigowa yana ta zuba murmushi..
Kallon shi tayi yadda ya zauna yana ta sake duba kwalliyar daya ciyo..
Dariya tayi a hankali kafin tace "base ka sake duba kanka ba,na duba maka kayi matukar kyau tamkar sarkin zinare"
Murmushin ya sake me cike da murna..a hankali ya kalle ta kafin yace "yunwa"
Bude baki tayi da Ido kafin tace "ban fa dauka da gaske zaka zo ba,so bayi Maka ba"
Ce mata yayi "Amman ai na ce din"
Kunnuwan ta ta kama alamun afuwa kafin tace "yanzu kuwa zan samo Maka abinci kaci"
"Indomie " ya fada da karfi,alamun da suka nuna mata da kyar maganar ta zaru ta fito daga bakin sa..
Kitchen ta tafi,kan wani lokaci ta dafo masa indomie da egg ga sausage a gefe me dadin gaske..
A wani jug Kuma zobo ne sansanya ya hade Rai se slow yake,se Kuma gefe flask ne dauke yake da tea me kayan kamshi Koda ze bukata..
Da yake ba me son tea bane , indomie kawai yaci yasha zobon da ta dauko masa sosai ya koshi..
Zaune shiru shi beyi magana ba ita ma haka..
A hankali yace 20 years back..
"Nazo gidan ki ran da aka Kai ki gidan mijin ki..kiyi hakuri ki yafe mun"
Taji shigowar message a wayar ta,ta San ma shine,se kawai ta dauka ta bude ta karanta,se tace
"Na sani,ya fada mun ,amman se a shekara ta 17 da auren mu sannan na sani,na wahala Kuma duk saboda zuwan da Kai ne "
Kallon ta yayi ganin yanayin da ta shiga kafin yace "Wahala Kuma? Wace iri?
Kallon shi tayi tana murmushi sannan ta rubuta masa "ai ya wuce "
Murmushin yayi mata ita ma sannan yace "bakya so na sani kenan? Shekenan naji,se yaushe yaran zasu dawo ne,mene sunayan su?"
Cewa tayi "se sanda Sarki ya Sanya aka maido su"
"Sarki Kuma,wani sarki?Su nawa ne ma ?"
Ya sake tambayar duk da ta message be Yana Yi Yana aika mata da kallon so..
Se tace "Abulkhairu,Zahra'u,Saudatu,Nabila se Asif da Arif"
"Maasha Allah,haka da yawa ? Amman naso ace nine baban su"
Murmushin tayi kafin tace"kaddara ta ruga fata"
Girgiza Kai yayi cikin Jin ciwon kasantuwar ta haihu har haka da wani ..
Kallon shi tayi tace..
"Ajje wayar ka Babban mutum,Ina so mu runga magana da baki,mene yake hanaka magana ne ma wai? "
Rubuta mata yayi "suna mun nauyi ne,sannan in na matsa se nayi magana ihu nake yi"
Murmushi tayi kafin tace masa ..
"Toh muyi kokarin saita ihun da zuciyar mu,sannan mu dage se munyi magana,dan in ba magana fa zan ce na fasa"
Zaro Ido yayi a hankali Yana kamo saitin zuciyar shi,se ga kwalla..
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...