(31)

44 7 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(31)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Daga wayar tayi ta Kara a kunnen ta ..

Saukar numfashin ta kawai da yaji,se yaji Wani lumana da natsuwa da farin ciki hade da Wani irin kwanciyar hankali sun zo Mai..

"Hello" yace

Shiru tayi,se ya sake cewa "a mun magana mana Zahra,nasan ana jina"

"Ina yini" aka ce Mai

Yace "yini Kuma,shin wai ko an bani ajiyar yinin nan ne da ake ta tambayar inda yake?"

Murmushi tayi me kayatar wa dan ta fuskanci shi baya amsa gaisuwar "Ina yini" Kai tsaye.

Cewa tayi "Toh barka da dare "

Se yace "Yauwa Yan mata,barkan ki dai,ya gidan?"

Cewa tayi "Alhamdulillah"

Se yace "shine kika ki daga wayan da nayi ko?"

Murmushi ta sake yi Kawai ba tace komi ba

Se yace "Dazu shine aka gudu aka barni a tsaye ko kamar Wani soja,ba komai ai,na gane ba'a Sona,zan hakura kawai na daina damun ki"

Cewa tayi " um um"

Yace "um um me?"

Se tace "nidai um um"

Murmushi yayi me cike da nishadi,sannan yace "toh ana Sona?"

Shiru tayi har tana rufe fuskar ta da pillow din da ta jawo daga kan yar katifar su ,Kuma a zahirin gaskiya ma bata san sanda ta dauko shi ba.

Asalin zakin soyayya ne ya kwashe ta  yasa ta janyo pillow din tana dan jujjuya shi a kan cinyar ta ba tare da ta sani ba..

"A dan daure a gaya mun mana"

Shiru ta mai,dama yasan ze yi wuya ace ma ta bashi amsa .

Se yace "toh shekenan,yanzu kin San me zamuyi?zanga patients dina,kina ji Muna waya se kawo files ake sun dan taru let me attend to them okay?..

Amman kafin nan zan sake tambayar ki ko ana Sona,in akai dropping wayar na san ana sona.in Kuma ba'ai dropping ba nasan ba'a Sona ..kin yarda?

Cewa tayi "umm"

Se yace  "toh ana so...".

Ai bata ma bari ba ya karasa ba ma ta kashe wayar ta tana boye fuskar ta yayin da bugun zuciyar ta ya karu da gudu gudu yake bugawa ..bum bum bum

✨💕

A gefen Sufyan kuwa, da yayi wani wawan juyi a kan kujeran shi ta likitoci se da ya fado kasa be sani ba ..

Tashi yayi Yana dan rawa Yana godewa Allah cike da farin ciki.

Gyara zama yayi sannan ya dafe zuciyar shi cike da Wani irin shauki ..

First patient din sa ne yayi knocking kofar,tuni ya koma serious ya nutsu sosai a kan kujera ..

Hand sanitizer ya matsa a hannun shi,ya murmuza sosai,kana ya Saka hand gloves din su na Dr's ya fara attending musu..

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now