SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(20)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Fitan Abida ta nufi motar ta ta kama hanyar gidan Uncle Baba da tunanin Abul dinta ko Wani Hali yake ciki?
Abunka da mota ba Wani dade wa se gata a gate din gidan ta shige ciki,lokacin misalin biyar saura few minutes.
Ta tadda su Uncle Baba sun dawo ,ta iske har an siyo wa su Asif baby milk da sabbin feeding bottles har an hada musu madaran sun sha sunyi dam dasu .
Da ta shiga gidan ta taradda Yaran ta sun sake suna ta wasan su.
Abul dai yana kwance kan doguwar kujera ya rufe ido kamar yana bacci,amman idon shi biyu.
Gun shi maman ta fara zuwa ta taba jikin shi,bayan ya bude ido ne yake cewa "Sannu da zuwa mama" ya fada yana me Jin kunyar ganin idon ta sanadiyar tuno abunda ya aikata ..
Cewa tayi "yawwa Yaya Baban Alkhairi,ya gida ince dai su Proff ba suyi ta hayaniya ba sannan Yan biyu basuyi rigima ba ?"
Sarai ta lura yana Jin kunyar hada ido da ita ne,ita Kuma se ta share shi tayi kamar ma bata gane Hakan ba.
Bata ma Jira Jin amsar da zai bayar ba ta juya ta wuce toilet.
Sallah ta tayar da yake tayo Alwala yanzu a guest toilet din dake a nan parlon.
Tana idar da Sallah Uncle Baba da Maman Amina na sauko wa daga sama ,tare da yan biyu a a hannun su..
Cike da fara'ah suke tarbar Abida wadda ita Kuma take ta yake saboda kuncin da zuciyar ta take ciki..
A mutunce take ta gaishe da su suma Kuma suna amsa mata.
Su Abul ma suka sake gaida su Uncle Baban sannan suka tashi suka shiga dakin da suka zauna a ciki dazu sakamakon Wani kallo da Maman ta musu ..Wanda yasa sun fahimci cewa ba'a bukatar su a gun.
kuma fa ba Wani mugun kallo bane,kawai da ido tayi magana se suka yunkura suka mike..
Da maman Amina ta lura kamar da magana a bakin Abida se Maman Amina tace "bari na leka naga su sahura ko sun kammala aikin ,daya daga cikin masu aikin gidan ce sahuran"
Tashi tayi da Asif a hannunta suka wuce kitchen.
Abida bata boyewa Uncle Baba komi ba ta gaya mishi.
Yaji tausayin ta,sannan yaji rashin dadin mutuwar auren ta dai dai gwargwadon adadin yadda Koda Usmanu Dan fodio ne keda rai haka zai ji.
Nasiha ya mata sosai wadda ya kashe mata jiki da ita sarai,sannan ya sake Bata hakuri,Kuma ya nuna mata alfanun yin hakuri a duniya,dan duk tsanani yana tare da sauki,sannan duk abunda hakuri be baka ba rashin shi ma baya baka..
Hakika Uncle Baba ya kashe mata duk wata gwiwa ta jikin abida da nasihar shi tare da ban hakurin Hadi da misalai daga mabanbanta bangarori,sannan yayi nasarar shaftare Kashi 40 na damuwar ta a wannan zaman da sukai.
Koda Maman Amina ta fito daga kitchen taji maganar da suke se ta wuce sama.
Uncle Baba ya bita da kallo dan son ganin yanayin ta domin tana Sako kafa Yana cewa .."Zaku zauna a nan ke da Yaran har muga Abunda Allah zeyi.."
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Genel Kurgulabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...