(47)

59 4 1
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(47)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Kuka ba na wasa ba Zahra ta sha a wannan rana me ruba zuciyar masoyi,ko amini.

Tun maman na jin tausayin ta,har ta komo yi mata dariya tana taba hannu,har ta koma Zarahn na bata haushi a karshen karshe dai,dole ta koma Jin tausayin yar ta ta..

Ba Zahra ta samu tayi bacci ba se wuraren 12 da ita da Maman ta da Abulkhairi..

Bayan doguwar nasiha gami da wa'azi tare da kwantar da hankali da ban hakuri ga lallashi wa Zahra..Amman Inaa har zuwa sanda suka tashi dukkan su sunyi jigum jigum saboda yadda Zarah ta koma kalar tausayi..

Kun tuno dama a cikin damuwar zuci take kwanannan ko? Yawwa toh yanzu me dalilin ne aka samu,dole a baje basirar kuka a gun..

A wannan zama na ranar,ba irin hakuri da ban  bakin da Maman bata ba ta ba,amman ga Zahra abun yaci tura domin ita ma kanta abun yahi karhin ta..

Se ta hakura se ta tuno wai za'a daura masa aure da wata,yar soyayyar da ya koyar da ita a taren su kenan akwai wata ita ma da zata dandani abunda ta ke ji?

Toh a nan ne labarin yake chanjawa ,se sabon kuka da bori,ga shi shi kan shi Sufyan din ya kira wayar ma anki a mai magana..

Allah sarki rayuwa ,ita fa soyayya haka take,ba abunda bata sawa ..gasu Zahra nan a yadda tazo musu,se muce Allah ya bamu sa'a baki daya a rayuwar mu..

💞✨💞

Sufyan ne zaune a office shi da Dr Danladi,se Dr Alhasan,aiki ne ya taso wa Danladi da Sufyan,Wanda suka samu Kiran gaggawa a garin na Kaduna domin duba wata tsohuwar mace wadda aiki za'a mata ma emergency..

Ya biyo ta fannin bangaren Su Sufyan,se dai gashi shi yau Alhamis ce,gobe juma'ah daurin auren su da Amarya Zahra .

A goben ne Kuma za'ai aikin,shine suke shawara akan Alhasan da Danladi suje shi Sufyan ya zauna,a lokacin se Danladi yake cewa Shima maman shi bata da lafiya tana kwance Kuma ita ma aiki za'ai mata,ya basu hakuri akan cewa baze iya kama wa Sufyan din ba kar kanshi ya rabu gida biyu ga patient ga mahaifiya..

Suka tsaida shawarar akan gobe bayan daurin aure se su wuce...da haka suka watse kowa ya cigaba da ayyukan sa a asibitin ,Allah ya kaimu gobe ..

💞✨💞✨

Ranar ta kasance ranar da ta kama ranar daurin auren ango Sufyan da amaryar sa wato Zahra'u queen..

Kamar yadda rana bata karya,toh hakan ne ya faru,an daura auren Amarya Zahra'u wadda suka tsufa a garin minjibir a park kamar yadda aka tsara ba tare Kuma da sanin Amarya ba..

Gun yayi musu dadi kwarai suka mance da  kunci da gajiya sukai ta wataya wa a fili ga teku da suka shiga boat cruise suka Sha shagali..

Bama abincin da sukai guziri da kayan dadi Wanda duk Sufyan ya tanaje su saboda tafiyar tayi musu armashi..

💞✨

Da misalin daya da rabi na ranar juma'ah dumbin jama'a suka shaida daurin auren Zahra da angon ta Sufyan .

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now