(11)

56 3 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(11)

_______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨✨✨
💞💞💞💞💞💞💞💞
✨✨✨✨✨✨✨✨

Kullum tana Kara Gode wa Allah da bata taba gaya musu ma ainahin yadda suke rayuwa a gidan ba,su dai sun San yana da kulle,ga Uban taurin Kai,se fada da kankamo .

Amman bayan haka sauran duk ta bar wa cikin ta.

Har fa fakar ido take yi ta danna ringtone din wayar ta da ya fara Kara se ta dauka ta fara wayar karya cikin raha da murmushi a zuwa da Baban Abul take waya.

Shi yasa mommy kan ce "Tunda dai yana sonta ai da sauki ma ba zallar masifar shi bace .."

Nan ko linke su take yi kawai a bai bai ..

Bayan Adda Muhsina ta gama sababin ta ta dauke ta a mota se wellcare.

Dama shopping zata je shine ta biyo ta gida.

Ahe rabon Abida ne ya rantse ta biyo ta gidan.

Kafin ma a tafi se da ta gaya mata magana ,cewa tayi "zo muje yawo in wannan masifaffen mijin naki ze barki .."

Murmushi tayi tana cewa "Kai Adda ze bari mana "

A ran Abida tace Wallahi ko zancen ma baze ji ba .tasan sarai in ta kira shi dan neman izini baze bari ba.

A wellcare dai Adda Muhsina cewa tayi "Bidallare ki dau duk abunda kike so kar kiji tausayi na zanje sama zan duba furniture ne .."

Da kwalla a idon Abida tace "Toh Adda,Amman dai Gwamma naji tausayin ki"

Ita Adda Muhsina tana ganin Babu a jikin Abida Kiri Kiri,ita Kuma Abidan bata San ana gani ba.

Dariya Adda Muhsina tayi ta wuce ta Haye sama abunta,da Kun ganta Kun San tana cikin Jin dadi da wadata har ma da kwanciyar hankali.

Dama Abida ta bar su Zahra a gida,hakan ya mata dadi sosai.

Dan haka se ta fara duba abubuwan da take ganin tafi bukata ,kamar su diaper , beverage's, biscuits ne da detergent se baby food wa Zahra da take hanyar tafiya wata 6 ko da ma se ta ajje kafin Zahran takai cin su ,Amman ba komai Gwamma ta ajje din.

Abubuwan yan kadan ta dauka,dan haka ta tsaya ta na Jiran Adda Muhsina ta gama su tafi ..

Ko da Adda Muhsina tazo  ta ga yan kayan kadan   se bata ce komai ba,ta fara nata shopping din Abida dai na biye da ita .

Yawan kayan da take dauka ba sabon abu bane a gun Abida a Asali.

Amman Kuma a yanzu kam se take kallon abun gwanin sha'awa da burge Dan ita rabon ta da zuwa shopping wai da kanta tun Bata yi Aure ba .

Suka gama Ko a wanchan lokacin da ake yayin iphone 5+ Kun San ba yau bane ? Toh ko a lokacin 150 thousand Adda Muhsina ta kashe ..

Abida se gwalalo idanun ta masu girma take yi abun na sake bata mamaki .hmm

Kai jama'a me wai ake da Sauyin rayuwa mara Dadi fisabilillahi?

Kiri Kiri Abida ta koma yar kauye,a zahiri ma gani take kayan sun yi yawa gashi dama wellcare tsadar kaya gare su,shi shago ne na manya dama .se taje ganin tsadar kayan.

Abunda zaka Siya a shagon unguwa dari daya a wellcare is 1000 .

Haka dai Abida da mamakin ta suka gama suka fito,se Adda Muhsina ta biyo da Su  ta sai musu pizza a pizza hut suka taho gida.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now