(17)

45 4 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(17)

_______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Da ta duba se taga da asara gwara gidadan ci,da ta dauke proff ta rasa karatun ta gaba daya Gwamma ta barta tayi karatun a gidan Uncle Baba,kawai ta fada mota tare da Yaran .

Su Abul aka sauke Wanda ya shiga ajin karshe na secondary suke taka matsayin big boys a school din,shi aka ma bawa head boy .Amman se ran Monday za'ai announcing din su a gaban assembly.

Malam sani da ya sauke su Proff a makaranta se ya wuce da Abida gidan Uncle Baba kamar yadda ta bukata.

Tabbas Basu tashi daga bacci ba ,shi yasa da ta karasa cikin falon se ta rabe daga gefe ita da Yan biyu kamar wasu maroka.

Se wajajen 10 sannan Uncle Baba da Maman Amina suka sauko .

Baiwar Allah har tayi bacci ita da Yan biyun ta.

Cikin sakin fuska suka tarbe ta tare da amsar Yan biyun daga hannun ta cikin sha'awar Yaran suna musu wasa.

Bayan an natsa har sun karya ita ma Abida an zubo mata alagwarje special wato farfesun ox tale da soyayyan dankalin Hausa gefe guda Kuma ga wainar kwai da shayi irin hadin kaurin nan ga butter nan in tana da ra'ayi.

Bata ha'inci kanta ba ta gyara zama taci tayi nat da ita,se dai duk Loma daya da take yi tana yin ta ne tare da tunanin Yaran ta da basu ci wannan dadin tare da ita ba.

Amman ba yadda zata yi dole ta ci dan kar a rasa gaba daya ..

Zaune Uncle Baba yake a kan rantsattiyar turkey couch din shi three seater,yayin da Abida ke zaune a kasa juyin duniya ta tashi ta zauna a kan kujera taki dole aka bar ta kasan .

Kallon ta yake yi yayin da Kuma yake jiran Jin me zata ce ,dan daga dukkan alamu sun nuna cewa akwai magana a bakin ta,se dai kamar yadda yake tunani haka din ne ,ta rasa yadda zatayi ta gaya masa abun da ya kawo ta.

Katse ta yayi da fadin"Abida akwai matsala ne?"

Dan gyara zama tayi tana Dan sake tunanin ta fada din ko kuwa Taki tayi kafin dai ta yanke shawaran cewa "Baba Baba tafiya nake son yi ne ,shine nace zan roki alfarman Saudatu ta zauna a nan gidan kan in dawo saboda makaranta "

Uncle Baba ba yaro bane,Amman se yaji zuciyar shi na Dan tantamar maganar tata,Kuma bawai Dan be yarda da ita ba,Amman kawai se yaji yana bukatar yi mata tambayoyi kamar haka..

Cewa yayi "Ah toh toh,tafiya zuwa ina?"

Dan diri diri tayi Wanda ya sake tabbatar da zargin da yayi na tantamar maganar tata..

"Uhm Ina jinki Ina Zaki?"

"Ka-kats um Kaduna zamu"

Jefo mata wata tambayar yayi da fadin "ke dawa"

Abun ka dame damuwa Kuma ta hadu da tsohon barrister se kawai ta rikice se hawaye sharrrr....

Shiru yayi Yana binta da ido yayin da Yan biyu je ta faman chakumar sa se kace Wani Uban su.

Kallon ta yake sosai yana son karanatar Wani abun a tattare da ita,se dai be iya karanto komai ba se tsananin damuwar da ta nuna a jikin ta ..

Wasa ya cigaba da yi da Yan biyu har zuwa sanda ta tsagaita da kukan tana sauke ajiyar rai.

Ce mata yayi "Abida kin dauke ni a matsayin marigayi usmanu Dan fodio?"

Daga Kai tayi.

Se yace "Toh Ina son ki gaya mun meke damun ki,ni Kuma Insha Allah zan miki maganin ta in dai wadda bata fi karfin na bace .."

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now