SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(35)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Sufyan tun daga wannan lokacin se ya zamana duk sati yake Kai wa mama cefane.
Tarkaccen kayan miya ne,nama,Mai.
Su kuwa su shinkafa an wuce gun,ya siyo karamin buhu,da carton din taliya, macaroni harda carton din indomie,ledar maggi.kai shopping rigijib jib dai yayi musu dab harda omon wanki,se sabulai na wanka duk seda ya siyo,man shafa wa sanitary pads,under arm duka dai.
Ya girgiza kam ba laifi,dan siyayyar da yayi ba ta wasa bace ba a dai wannan zamanin,musamman yadda al'amuran rayuwa suka sauya komai ya tsefe,toh amman ai da yake yiwa Kai ne ,Kuma wannan be Fi karfin sadaqah ba ko?
✨💕✨💕
A gefen su Soffy kuwa bayan malam ya tafi ne ake sake Hamdala ana godewa Allah me kowa me komai.
Anan se soffy ta nemi alfarmar Dan Allah su daddy da mommy kar su gaya wa kowa ta dawo gani,saboda tana son tasan masu son ta dan Allah,musamman Yan uwan su da soffy ta ruga ganin yadda suke mata kallon kyama da take da makantar karyar ta ..
Su mommy suka yadda se soffy ta cigaba da karyar makantar ta..
✨💕✨💕
Da daddare Kuma ta gefin fagge..
Hannu Uncle Baba ya mika wa Sufyan suka gaisa se ya janyo sa gefe ..
Ya ce "saurayi sannun mu, ya sunan ka?"
Cike da mamaki Sufyan ya amsa da cewa "Sufyan Sunana "
Cewa Uncle Baba yayi "naga ka fito daga gidan chan,wato gidan su Abulkhairi,jiya ma kamar haka naga tafiyar ka daga gidan,shin in ba damuwa zan iya sanin dalilin da yake kawo ka nan din?"
A take tunanika da yawa suka darsu,sannan Kuma suka watsu a zuciyar Sufyan ya hau barbaza su sassa sassa dan fayyace me yake so ya gane ..
Tunanin shi ya bashi cewa duk yadda akai mutumin nan nada alaqa dasu Abulkhairi da har yake masa tambaya,dan in ba haka ba ba dalilin da zesa kawai Wani ya tsare shi ya kama yi mai tambaya akan dalilin zuwan shi Wani guri gaba daya ma.
Tunda tun sanda ya fara zuwa ba wanda ya Wani taba Mai tambayar dalilin zuwan sa,se fa yau .
Da yake Shima Sufyan din yana son sanin Wani abu game da su Zahran,musamman whereabouts din mahaifin su, se yace
"Ni ne me neman auren Zahra,dama kwanan nan ma nake so zan turo manya na"
Dan murmushi uncle Baba yayi sannan yace "Ba shakka ,naji dadin ganin ka,duk da ko ba jima ko ba dade se an neme ni sannan za'a baka auren Zahran,tunda ma Allah yasa mun hadu ai shekenan,abun yazo da sauki,yanzu se ka amshi number ta,daga baya se ayi maganar,ni ne mahaifin su Zahra"
Tuni Sufyan ya warce hannun sa daga ruqon da Uncle Baba yai mishi har Yana russuna wa uncle baban cike da Jin kunya da farin cikin ganin Baban masoyiyar sa..
Murmushi Uncle Baban yayi se yace
"Amma fa ko ita Zahran kar ka nunawa mun hadu,balle maman tasu ma ta sani,akwai lokacin da zan zo gare su kaji malam Sufyanu?"
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...