SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(40)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Da sallamar shi ya shigo yayi fes ga Wani fresh da fuskar nan tayi se baza Wani sassayan kamshi Wanda ya dace da yanayin safiyar da aka waya ga dadin kamshi ga Sanya nishadi da nitsuwar zuciyar yake yi.
Baya ga haka Kuma Indai akwai masoyiya a guri da ta shaki kamshin nan zata ni'imtu da shi sannan ta Sanya a ranta cewa musamman dan ita gwanin nata ya sanyo wannan turaren me kamshi irin na alfarma..
kamshin fa sooooo coooool gashi irin mild din nan..
Oga sufy,Saye yake da wata haddadiyar Moroccan jallabiya dinan..
gefe guda ya samu ya cire takalmin sa da ya kasance Crocs irin authentic Crocs dinnan dan 25-30k ,ga shi daman shi Sufyan yana da dabi'ar Saka socks,a yau ma saye yake da guda daya ita Kuma kalar ruwan toka kamar yadda kalar Crocs din ya kasance hade da kalar jallabiyar.
Yayi kyau kam,dan dama Sufyan kam ba baya ba gaskiya.
Cike da so da kauna tare da girmamawa ya zauna yake gaishe da Mama tare da tambayar karfin jikin nata take cewa "Jiki ya samu kulawar likita,yaji sauki sosai Alhamdulillah"
Mafi akasari daman tafi Kiran sunan shi da likitan a maimakon Sufyan din ..
Su Nabila ne Suma suka gaishe sa cike da murnar ganin shi,twins kuwa dama tuni sun zauna gefe da gefen sa suna zayyano tambayar mutan gidan su Sufyan din da suka baro cike da marari da kewa..
Murmushi yake yi yana ta amsa musu cike da kulawa abun gwanin sha'awa.
Dama suma yan biyu da hikimar su suke magana,basa irin hira kaji suna shirme kamar da yara kake yi,suna da wayon su kam daidai gwargwado kamar Uban su..
Zahra dai tana daki tunda taji zuwan shi,ko ba komai ita dai tana jin kunya,ga shi Sufyan da iya tsare mutum da ido idan yaso baya kunyar zaman maman su a wajen,se ya Saka ta tayi ta Jin kunya ita..
Tiren da aka jere wa Sufyan kosai da kokon mama ta sa Asif ya ajje a gaban Sufyan bayan nan Shima yaje ya jawo musu nasu shida Arif ya maido kusa da Sufyan ..
Nabila da mama suke cin nasu Suma.Se Abul da suke dan taba hirar makarantar su da oga Sufyan,yake cewa gobe ze koma school ma shi..
Kallon kowa na cin abincin banda sarauniyar zuciyar sa hasken idaniyar sa fitilar dukkanin duhun sa ne yace ..
"Dr Ina Addar ku?"Se da Nabila ta Kalli kofar dakin nasu sannan tace " tana cikin daki"
Cewa Nabila yayi "jeki kice tazo yanzu"
Tashi Nabila tayi ta nufi gun Addar su kamar yadda sufy yace ,ta isar mata da sakon sa.
Murmushi Zahra ta saki Jin ya aiko a kira ta..
Tashi tayi ta fito tana rabe rabe se kace wata dagangare ta fito daga dakin saye a cikin ire iren kayan da Maman su sufyan suka basu, atamfa ce dinkin riga three quarter da straight skirt.tayi kyau matuka,abun ku da kyakkyawa dama
Ta gefen idon sa yake kallon ta yayin da yaga tayi masa kyau dai dai gwargwado,tana ta tashin annuri..
Cikin zancen zucin sa yaji tana cewa "Ina kwana ya "
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...