PAGE ONE

1.1K 25 11
                                    

         Ouummey

page 1️⃣

_____________________Da ƙarfi aka buga ƙofar ɗakin tare da shigowa, a dan firgice na dago kai na daga sunkuyar da shi ɗin da nayi, sedai Kafin nayi wani yunkuri tuni naji an rufe ni da duka

"A'a a'a, kai Safiyya, me yasa bakya jin magana ne".

Fadin yaya tana kokarin hana  Mama dake amsa sunan Safiyya dukana.

"Ki bar ni yaya, ki bar ni in sabauta yarinyar nan ko zan ji sanyi a raina, wannan wace irin ƙaddara ce, ka haifi da a cikin ka ya zame maka musiba, wallahi ina nadamar haihuwar yarinyar nan, da na sani da tun a ciki na zubar da ita na huta da bakin ciki".

Yayah  ta janye Mama tana fita da ita daga ɗakin

"Ki dena fadin irin wannan mugayen kalaman kan yar da kika haifa da cikin ki dan kin san bakin uwa, ki kuma yi hakuri ki daina wannan kukan dan ba abinda ze kara face musiba ga rayuwar ta yau ace mahaifiyar ta na zubda hawaye akan ta".

"Banni Yayah, banni nayi kuka, tun fara girman NU'AIMAH take kunsa min takaici kala kala, ban da bakin ciki babu abinda na amfana da shi a rayuwar yarinyar nan, wace irin soyayya ce ban nuna mata ba, wane irin kauna ne ban gwada mata ba, a duk cikin ya'yan da na haifa wa na so na kauna kamar ta, wa nai wa gatan da nayi wa AIMAH?, amma kaf cikin su ita ce kadai me bakan ta min rai, ki fa duba irin tashin hankali da gwagwarmayar da ta saka ni shekara biyar zuwa uku baya, shine kuma duk be ishe ta ba se ta sake wani yanzu? Kashe ni take son yi ko me, wai Allah ni Safiyya na shiga uku".

Ta kai karshe tana sake rushewa da kuka,

"Koma dai ya faru a baya fa har da laifin ki Safiyya, ko da laifin AIMAH amma zan iya cewa naku ya fi yawa dan kuka bata dama ku ka sakar mata kuka kuma sangarta ta shiyasa ta taso a haka, se kuma daga baya kuce zaku gyara ta, bayan shi ice tun yana danye ake tankwara shi, in kuwa ya girma aka ce za'a tankwara sedai ya balle".

Ajiyar zuciya Yayah tayi tare da riko hannun Mama

"Kiyi hakuri da yanayin ƙaddarar ta Safiyyah, ki kuma koyi yin kyakkyawan kalami a kan ta, ina ji a jikina komai yazo karshe a wannan lokacin Insha Allah".

Zare hannun ta tayi daga na Yayahn

"Na dade da zare Aimah daga cikin addu'a ta dan ba lafiyar ƙwaƙwalwa ce bata da ita ba balle ace ai bata san daidai ba, haka kuma ba aljanu gare ta balle ace she's possessed, kawai tsabar iskanci da jin ita ta tsaga ne dan haka na bar bata lokaci na wajen mata addu'a tunda Allah ai ya azurta ni da wasu ya'yan bayan ita, taje tayi rayuwar ta duk yadda taga zata iya sedai ɓacin ran da take sani da damuwa da sannu itama zata haifa kuma zata gani, Abu daya na sani shine wallahi se na raba wannan kaddararren auren tsakanin ta da MASDOOQ, dan shi ɗin ya fi karfin ta, ba sa'an auren ta bane dan haka se ya sake ta taje ta naimo daidai ita".

"Ashe baki da hankali Safiyya, auren da aka ɗaura ɗazu ɗazu kike maganar rabawa?".

"Shi dai Yayah, ashe ma in na bar auren taci riba kenan, bayan duk abinda tayi a baya kina tunanin ta dace da samun irin wannan damar ne?, Sam wallahi dan haka kar ki ma fara ce min in dakata Yayah dan a wannan karon ba zan ji ki ba".

"Nima kuma ba zan saurari haukan ki ba dan haka auren Aimah da Masdooq ban ga wanda ze raba shi ba ko da kuwa shi ɗin da kan shi ne".

A mamakan ce Safiyya ta kalli yayar tata

"Kar ki yi haka Yayah, kar ki fara fadar haka, kar ki sa zuciya ta ta fara saka min tunanin dan Masdooq yana dan ki ne yasa kika fadi haka Yayah".

"In har haka zuciyar ta ki ta saka miki to ki dauke shi as hakan, dan na gama magana, Aimah ta zama matar Masdooq and ba zan yadda da duk wani matsala da zata shigo tsakani ba".

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now