Ouummey 031
Page 3️⃣1️⃣
___________________Hawayen da ban san na meye ba suka shiga tsere kan kunci na, baki na ya shiga bari amma na kasa cewa komai, har lokacin kuma idanun mu na sarke cikin na juna, in na rantse ba zan yi kaffara ba a wannan lokacin hatta zuciya ta se da ta tsaya da beating, agogo ya tsaya da bugu, lokaci da komai ya tsaya da tafiya, babu abinda yake motsi a lokacin face Aimah and Masdooq, only the two of us.
Na shiga lumshe ido na very slowly, se kuma lokacin zuciya ta ta dawo da bugu, se tsalle take a kirji na looking for something I knew not, sassanyan harshen sa ya sauka kan kunci na wiping away my tears, na kankame hannun sa batare da na san nayi ba, haka kuma take tears din suka kame kamas, yana kai wa saitin ido na ya sunbace idon cikin wani irin soyayya me karfi da tsafta, ya hade fuskar mu, goshin mu kan na juna, hancin sa kan nawa, lips din sa na brushing nawa haka muna exchanging breath,
"Barbie, If you ask me about love, I can’t answer you but if you ask me who I love, the answer is you and will always be, life can give us lots of beautiful persons, but only one person is enough for a beautiful life, and you're my that one person, stay in my life, forever Barbie, will you Please????".
Jin da gaske numfashi na na neman daukewa yasa na fisge jiki na tare da juya masa baya, hawaye na bin kunci na daya bayan daya, ina jin shi ya sake matsowa ya kwantar da kan sa a baya na batare da ya sake cewa komai ba, haka muka yi shiru tsayin lokaci, ina jin hucin numfashin sa dake sauka a baya na, har se da na ji na saisaita nutsuwa ta, nasa hannu na daga kan sa a hankali na saukaa daga bed din gaba daya, se lokacin muka sake hada idanu, na sunkuyar da nawa da sauri dan se na ji ina jin nauyin sa a yau, kunyar hada ido nake da shi, shi kuma kamar ya fahimta se ya sauko shima ya tsaya gaba na tare da rike hannu na
"Wil you pls try giving 'US' a chance?, I promise you won't regret it".
Kai na na kasa na bude baki nace
"It's not like I don't love you sweetheart, Allah ya sani ina son ka ina kaunar ka, but a matsayin yaya na not my husband, the love I have for you ba na soyayyar aure bane, wannan Ibrahim nake yi wa, but Please give me some time, ka bani lokaci nayi digesting all that happened, yanzu ji na nake blank and empty , komai sabo nake ganin shi, ina bukatar lokaci nayi tunani and decide our fate, sedai I promise you khair insha Allah".
Gyada kai yayi alaman ya fahimta, se ya sake ni ya shiga toilet, ya dan jima sannan ya fito, lokacin na koma na zauna bakin bed,
"Ga ruwan wanka nan na hada miki, take your bath, I'm coming".
Daga haka ya fita, na raka bayan sa da kallo cikin tunani, kafin kuma na aje komai a gefe na shiga rage kayan jiki na sannan na shiga toilet.
Har na fito be dawo ba, se na buɗe wardrobe da su Aunty Luba suka min jeren kaya na, sedai to my utmost surprise komai na ciki sabo ne, elegant and classy, na shiga bin kayan da kallo cikin mamaki dan nidai na san ba'a min lefe ba, ko da yake ba na ce ba dan ba'a sa ni a cikin komai da ya shafi auren ba kamar ba aure na ba.
A hankali na koma bangaren sleeping wears, suma dai gasu nan birjik kala kala kaman zasu yi magana, kowacce gwanin sha'awa, na rasa ma wadda zan dauka, daga karshe na dauko wani pink color riga iya cinya da wandon ta da yake tsayawa daidai tsayin rigar.
Na saka tare da yin wanka da turare kamar yadda na saba, na gyara gashi na na saka hulan bacci kana na saka pink socks da ke tare da kayan na kara karfin AC na kwanta tare da jan duvet na rufe jiki na, tsayin lokaci ina so na yi bacci amma tunani ka sun cika min kai, a haka ya shigo ya same ni, shima yayi wanka ya saka kayan bacci sa farare, yayi kyau sosai, ya tako zuwa bakin bed ya zauna tare da duba na
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
Ficción GeneralSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...
