Ouummey 033
Page 3️⃣3️⃣
______________________Dariya nake hakwara na a waje, ina ta shafa mara ta kamar me shafa baby, kaunar sa na sake ratsa ni.
"I know ko kowa ze kini ban da kai baby na, na sani ko ban samu adalci a wajen kowa ba ban da kai, i knew I've wronged your Dad and my family, I've cheat him, nayi masa abinda be kamata ba, but ai ba duka ba ne laifi na ko? Starting with Mama, eh mama has the right to be angry with me tun da ta fada min abu naki ji, ta roke ni na bijire, na saba umarnin ta na bakanta mata, amma kafin nan ai suna da laifi ko?, Ba'a raine ni kan nema in rasa ba, ba'a koya min cewa a rayuwa akwai samu akwai rashi ba, samu kadai na sani ni, kome nake so yi min ake tun daga yarinta har girma na, me yasa kuma se daga baya za'a ce min akwai abinda zan iya rasawa, bayan na san na samu duk abinda nake so, shima kuma a lokacin ina ganin in na dage zan samu?.
Bayan wannan, ilimin addini na a lokacin is not that much, bana san zuwa islamiyya kuma Mama ta goya min baya, Ya Salman da yake kokarin ganin ya tsaya a gare ni Mama ta katange tsakanin mu, ban manta irin tijarar da Mama tayi masa ba, a lokacin se da ya zama na in nayi masa magana harara ce amsa gare ni saboda bacin rai, kafin ya dawo ya saki ya cigaba da bin mu da addu'a kawai. Ya Farooq ma da ya dawo da karfin sa ya tsaya kan tsawatar min daga karshe har gidan Mama ta hana shi shigowa, Ya Najeeb ma haka, tsakani na da Ya Ahmad ne kawai bata shiga ba saboda shi me sanyi ne gare ni, tsakanin mu nasiha ce kawai.
To me yasa kuma daga baya zata ke ganin laifi na, bayan tushen komai ya faro ne daga gare su?.Abba, Allah ya jikansa da rahama ba zan iya cewa wani abu a kan sa ba, na yafe masa ya yafe min, duk da cewa alkhairan sa sun fi komai yawa gare ni, be sangarta ni kamar Mama bq dan shi be san bana zuwa islamiyya ba, haka duk da baya min fada ko duka amma yana min nasiha, cikin nasiha yake fada min abinda yake so na yi da wanda yake so na bari, se dai ya sabar min da komai nake so ze yi min ko ze siya min, har yau ban daina kukan so da kauna tare da kewar Abba na ba, na san duk da yana raye da ba'a banzatar da ni haka ba, ko kowa ze yi fushi da ni ban da shi, Allah ka jikan sa ka rahmata masa kasa aljanna ce makomar iyayen mu baki daya".
Na karshe ina fashewa da kuka, wannan maganar da nake yi ba karamin raunata zuciya ta take yi ba, abu ne da ya dade ya jima a raina na kuma rasa wa zan furta wa, ko da Huzaifa ya kasance malami na kuma ya san wacece ni ba wai yana nufin komai kuma da ke faruwa ina fada masa bane, daga labari na ban kuma sanar da shi komai da ya dangance ni ba, ba shi kadai ba, kowa ban sanarwa ba, na bar abin a raina ne tsayin wannan lokacin ina fama da nauyin sa, yau daya da na rage se nake jin na samu sassauci kadan na nauyin da zuciya ta ke dauke da shi, haka nauyin da nake jin tayi min q kirji na shima ya ragu.
Se da na sha kuka na na koshi, wanda da ace hawaye na karewa a idon mutum to da na jima babu sauran digon ruwa a idanu na saboda kukan da nake yi a kwanan nan.
A hankali na yunkura na mike, saboda nauyin cikin a cinya ta da kafafu na nake jin sa, shiyasa tashi da tafiya su ke ban wahala.
Wardrobe na bude na jawo gwangwanin madara Nido, cikin sabuwar siyayyan da Ya Masdooq yayi min na watannan, dan yanzu duk wata yake kawo min siyaya, indomie, kayan tea, kwai, Bama, bread, snacks, custard, cornflakes, cooking oil, juices, ruwan gora da gas dina dan karami, shiyasa ban da matsalar abinci ko yunwa, abinci me nauyi ne kadai ake kawo min daga wajen Sa'adah, wanda lokuta da dama Bama ci nake ba, saboda tun ganin madara se naji babu abinda nake so kamar madarar, shiyasa se na hada da bournvita ko milo na yi ta shan kaya na, wataran ma madarar ce kawai se na saka ma ta suga kamar dai yadda nake kokarin yi yanzu.
A dan bowl me madaidaicin girma na hada na sakan tea spoon na dauko ruwa da bread na koma bakin bed na zauna, yau kam bayan na gama hada madarar cikin bread na dinga zuba madarar a tsakiyar bread ina cin abi na, kun san me, da ruwa na dinga kora shi, babu damuwar sanyin sa balle, kai ciki masu gari.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...