PAGE FOURTY THREE

482 19 2
                                    

Ouummey 043

Page 4️⃣3️⃣

__________________Tun daga ranar ba wanda ya sake shigowa inda nake a cikin su, ni dai na ga an canja min daki, ban damu ba dan ina kankame da ƴaƴana a kirji na aka tura ni a kan bed zuwa dakin.

Nurse Vanessa, wata Christian ita ke kula da ni da Babies di na ita da sister Husna, itama nurse ce, se Dr da kan shigo sa'i da lokaci ya duba ni.

Masdooq kam kullum yana zuwa, da asuba da kuma dare wajejen 12pm, duk yazo se a nannada kaya suyi kamar baby a sa a showel dina da nake dora hannaye na, ni a nawa wautar na danne su yadda ba wanda ze zo ya dauke min, se a kai masa yaran office din Dr, wanda saboda Masdooq yake zuwa kullum by 11:30pm.

A haka yayi naming din su, the baby boy sunan Abba, wato Muhammad Bashir, macen kuma NU'AIMAH, wato suna na.

Ba wanda yayi expecting haka daga gare shi, kowa zato yake ze saka sunan Aunty Luba, Hajiya Yayah ko Mama ne, se gashi ya bada mamaki.

Hatta yan Barka da ke zuwa gida wajen Mama da Hajiya Yayah in suka ji sunan yarinyar se sun sake nanatawa kafin su share, a cikin iyayen mu kuwa ba wanda yayi masa maganar me yasa yayi haka.

Ya Farooq dai ne ya dube shi ranar da suka je office din tare, ranar da ya sakawa yaran suna

"Me yasa zaka saka sunan Aimah? Bayan ga sunan iyayen mu da suka fi cancanta ka saka?".
Ya Masdooq na cigaba da kallan Babyn yace

"Bana tunanin akwai sunan wanda ya fi nata cancanta da yarinyar nan, ko ka manta ita kadai ta raini abar ta taɓa ciki batare da taimakon kowannen mu ba, har kuwa da ni da nayi cikin?, Ka san wahalhalun da ta sha yayin zama da cikin, all the pains, the agony and the sleepless nights, all the tastelessness, abubuwa da yawa da ba mu sani ba, ta gama tazo haihuwa ta wahala, aka yanka cikin ta aka ciro Babyn, sannan take kan shayar da ita daga jikin ka kace bata yi deserving a sa sunan ta ba?, Beside all this alƙawari ne nayi in dai na haifi ƴa mace kuma na mata huduba da kai na to tabbas sunan ta Nu'aimah, se kuma God so kind ya sa Babyn ta zama her replica, what would I asked more?".

Cikin tausayi, mamaki da al'ajabin irin soyayyar nan Farooq yace

"Kana nufin after all abinda tayi maka a baya ko da bata dawo gare ka ba se ka haifi ƴa da wata matar ka saka mata sunan ta?, To what about princess? Me yasa ita kasa sunan Mama?".

"Ban taba rike Barbie a raina ba, ko da so daya kuwa, Allah ne shaida tun ranar da na furta mata saki rana bata fitowa ta fadi dare yayi gari ya waye batare da na ambatar wa ubangiji ya yafe wa Aimah ba, dan Nima na yafe mata, Farooq zaman mu da Aimah a wannan auren ba zama ne irin na kowane ma'aurata ba, na yi mata abubuwa da dama, na hana ta serving dina abinci, daga karshe na hana ta dafa min abincin ma, bana kwana tare da ita a same bed, duk da cewa ban taba daukar kwanan ta na kai wa Sa'adah ba, hakan ne ma ya kawo rabon yaran nan dan na shiga matsuwa sosai kuma ya zamto a ranar kwanan ta, i can't go to Sa'adah dole na daure komai na samu nutsuwa da ita, after that babu abinda ya kuma haɗa mu, ban matsar ta balle na san matsalar ta, seda ta kai ta kwanta a asibiti na kwana uku saboda yunwa, se kuma lokacin na gane nayi sakaci akan hakkin ta na ciyarwa, and from then ban kuma dauke ido daga kan abincin ta zuwa lafiyar ta ba, ban san me yasa ta zabi boye min tana da ciki ba, na dai lura daga baya kullum na shiga duba lafiyar ta zan same ta sanye da hijab ne, na tambayi kai na hijab din na meye, se kuma zuciya ta ta raya min tana kokarin killace jikin ta ne dan kar ya bani sha'awa har nace zan yi wani abu da ita, wannan tunanin yasa na daina kare wa jikin ta kallo, sedai na kan kalli fuskar ta sosai dan gane akwai ciwo tattare da ita ko da bata furta ba ko kuwa babu, ashe ciki ne da ita, and ban gane ba se ranar da na dawo daga tafiya na samu tana nakuda muka taho asibitin nan,hmmmmm".

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now