Ouummey 024
Page 2️⃣4️⃣
___________________Ban san ya samu Abba da batun magana ta da Ibrahim ba, se after three days, shima kamar kwanan baya Abba ya kira ni, ko da naje na same su shi da Mama se sweetheart.
Tun da na shigo nake sakin Murmushi ina kokarin mu hada ido, sedai tun da ya kalle ni so daya ya dauke kai ya maida kan Tv dake aiki, ganin haka se na karasa shigowa kuma direct wajen sa nayi, na zauna gefen sa har kafadar mu na haduwa.
Ban ji komai ba duk da ga su Abba a wajen se shine ya matsa a dabaran ce, na dan tabe baki ina tunanin irin halin shi, ko dai banza ai yasan ni kanwar sa ce ko.
A jimlance na musu sannu, shima kuma shi ya rada min kasa ƙasa yace na fada, Abba da Mama suka amsa kusan a tare, kana Abba ya gyara zama yana sakin Murmushi dan kuwa yaga san da yayi min magana.
A nutse ya kira suna na, na amsa tare da dagowa na kalle shi, se yayi pointing Ya Masdooq
"Yayanki ya same ni da maganar Ibrahim, yayi min maganganu masu nauyi da suka sa na sassauta zuciya ta kan batun, haka kuma na yarda na amince zan yi azumin kaffara kan rantsuwa ta, ba domin komai ba se dan na amince da bashi dama a karo na karshe kan batun ku ke da Ibrahim din, na baku seven months nan gaba yazo ya nemi auren ki, zuwa lokacin in har yadda kika fada ne matar sa ta haihu har ma baby yayi kwari, akasin haka kuma zan aurar dake out ga duk wanda hankali na ya kwanta da shi, kin amince?".
Zufa naji tana tsattsafowa a goshi na, ba dan komai ba se na kokonton amincewar da nake ciki, in na amince kuma aka zo Ibrahim be aiko ba lokacin ko aka samu wani akasi daga gidan su shikenan Abba na nufin aurar da ni ga wanda ban sani ba be sanni ba kuma wanda bana so shima kuma na san ze zama baya so na?.
Wani tsagin zuciya ta ke ingiza ni na amince, dan ya zuwa lokacin na san Ibrahim ze aiko, ai dama plan din mu is matar sa ta haihu kuma a dan kwana biyu ko, to ai lokacin ze zama ma baby na da wajen four months fa, then why the contemplating?, Kawai na amince mana!.
Ba tare da tunani ba na amince da gurguwar shawarar wannan bangare na zuciya ta, shawarar da ta zama silar kawo mu bigiren da muke kai yau.
"Na amince".
Abba ya dube ni sosai, duba na tsanaki kafin ya sake tambaya ta
"Kin amince?".
"Na amince".
"Kin amince?".
"Na amince".
A karo na uku ne kafin ya tambayi amince wa ta ya sake jaddada min fa babu bugu babu ja da baya a gaba, kar nazo na ce ban san zance ba
"Wallahi summa tallahi ba zan yi kaffara ba a gaba, in har Ibrahim be zo neman auren ki watanni bakwai ba masu zuwa se na aurar da ke ga duk wanda ya kwanta min, just consider this as kamar ranar aure ne na sa miki, coming seven months, ban san zancen hakuri ba, ban san neman alfarma ba, shin kin amince da sharadi na Nu'aimah?".
Wannan karon ba karsashi kamar a first and second round na furta amince wa ta, se kuma da na amsa sannan nake jin anya ban tafka kuskure ba, me yasa ban nemi Abba da ya bar batun sharadi ba kawai ya karamin lokaci, sedai ba yadda na iya, bakin alkalami ya riga ya bushe!.
Abba ya gyada kai cikin gamsuwa, kana ya dubi Mama da Ya Masdooq dake zaune a falon yace
"Ina fatan zaku zama shaida kuma alkalai a nan gaba, a gaban ku na fada mata sharadi na ta amince dashi, ina fatan Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi ".
Da Ameen suka amsa masa se Abba yace in tashi in je ya sallame ni, Ya Masdooq na kokarin tashi Abba ya kalle shi
"Fatan kai ma ka dinga tunawa da alkawarin da ke tsakanin mu".
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...