PAGE FIVE

207 9 1
                                    

Ouummey 005

Page 5️⃣

_____________________Ina nan zaune cikin rashin sanin abin yi har na ji fitar me gidan, ko da na duba time it's to eleven, ban yi mamaki ba sanin dama baya fita da wuri duk weekend, yanzu haka fitar da yayi ba office za shi ba gidan Hajiya Yayah ne za shi gaida su kamar yadda ya saba.

A baya dai na san bayan azahar yake dawowa gida, daga nan kuma baya sake fita se yin sallah kadai, duk da irin wulakanci da nuna masa ban san ganin sa da nake yi be sa ya fasa zaman gidan ba.

Wasa wasa ina nan zaune har aka kira azahar, na mike nayi na kuma komawa na zauna, rashin abin yi yasa gaba daya tunani ke neman yi min yawa.

Ina so in fita falo sedai ina jin kunyar hakan, ba wai kunyar Sa'adah ba, a'a kunyar kai na da kaina nake yi da kuma kunyar me gidan ya dawo ya same ni, da ba dan haka ba ai da ko kallo ne naje na yi dan korar tunanukan dake neman addaba ta.

Daga karshe se kawai na jingina da jikin bed na shiga takarar karatun Alkur'ani, a nutse nake karatu na da murya ƙasa ƙasa dan kar in damu me gidan, bayan haka ma kuma ga waka da na ji sun kunna ita da yan uwan ta da suka zo ne ko kawayen ta ban sani ba, sedai ina jin shewar su a falon tun dazu.

Ban yi tunanin dama ganin wani yazo waje na ba daga vangaren Mama har zuwa na Abba, balle kawaye da tuni na watsar da kowa, sedai ban yi tsammanin ba za'a aiko min da kayan sawa na ba, dan ban san yadda zan yi rayuwa ba kaya ba, se ga shi har close to sallar magrib ba wanda ya dube ni da batun abinci balle kuma kaya.

A haka aka kira magrib din na tashi da kyar duk jikina ba karfi, irin yadda kwana biyu nake faman wahaluwa da yunwa ban taba samun wannan matsalar ba a kaf rayuwa ta.

Duk yadda Mama ke jin haushi da yin fushi da ni bata taɓa min horon yunwa ba, abinda tace shine kawai ba zata dafa abinci ta bani ba, wannan yasa kafin ta zo yin girki ko ta gama zan shiga kitchen in dafa duk abinda nake so dan bata min iyaka da abinda zan ci da kuma wanda ba zan ci ba.

Gaba daya a kwana dayan da nayi gidan Masdooq na yi wani iri dani, idanuna sun yi zurfi zuru, haka sun dan fada sedai ban da su babu abinda ke nuna wani canji a tattare da ni.

Se bayan na idar da sallar magrib sannan yar aikin dai ta sake kawo min abinci, yanzu a cikin wani plate mara zurfi, abincin kuma iya tsakiya.

Ban yi korafi ba na karba da godiya na a aje a gaba na na shiga nazari, in na fahimta na kuma gane Sa'adah na neman yi min horon yunwa ne, a wuni ba'a ban abinci ba in an tashi a kawo min wanda aka san ko kwatar isa na baze yi ba, wato dai kora da hali take neman yi min.

A sannu na girgiza kai ina sakin wani busasshen murmushi mara armashi, lallai Sa'adah bata gama sanin wace ce ni ba, sa'ar ta daya ta samu mata sun yi laushi, da ace a da da nake amsa sunan Aimah ne da tuni wani zancen ake ba wannan ba, sedai a yanzu da na koyi rayuwa zan yi hakuri in zuba mata ido, duk abinda ta zo da shi in har be zama da cutarwa ba zan karbe shi in yi manage din rayuwa zuwa sanda Allah ze yaye min wannan jarabawar.

A hankali na jawo abincin nayi Bismillah na fara ci, tun a lomar farko hawaye ya cika min fuska na kuma hadiye da kyar saboda irin gishirin da aka cikawa abinci, ni ba wani abinda zan ci ba balle na hakura da ci, haka dole na dinga tura shi, dake ma ba yawa ne da shi ba loma biyar nayi ya kare.

Na ture plate din gefe na tashi na wanko hannu na na dawo na zauna, kawai se kuka ya kwace min, na shiga rera shi a hankali, daga yadda sautin sa ke fita duk me saurare na ze san ina cikin severe pain, Ina cikin radadi me zafi a raina da rayuwa ta, sedai bayan kukan babu abinda zan iya yi.

Abin ne ya hade min goma da ashirin, tuna Mama na gadon asibiti domin ni yana damuna matuka, haka na yi ta kuka har aka kira Sallar Isha, na tashi na yi ta na sake komawa na zauna.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now