Ouummey 018
Page 1️⃣8️⃣
___________________walima aka shirya wa su Ya Masdooq da za'a gabatar a gidan Baba, it's more like a family get together dan families din mu kadai aka gayyata, familyn su Mama, familyn Baba se kuma na bangaren Abba.
Karfe biyar aka tsara za'a yi taron, tun karfe biyu na tafi wani babban bakery da nake zuwa ina musu aiki two days in a week, dan na fada muku fa, cooking is one of my favorite hobbies, wannan yasa Mama ta tafi tace in na gama na taho.
Na so direct daga can in tafi gidan Hajiya Yayah, sedai tunanin za'a cika gidan yasa na ji na fasa, na wuce gida na yi wanka da ruwan dumi da ya ji turarukan waka masu kamshi da dadi, sannan na fito daure da towel.
Kan mirror na zauna na saka another clean towel na goge ruwan jiki na, duk da kuwa be wani zauna sosai ba kasancewar glass skin gare ni, ina gamawa na shiga mulke jiki na da mayuka na da are more of perfume saboda kamshin su, na shafa wanann na sak mulka wannan har dai na gama, na dawo na shafe tafin kafa na da nashi man, haka palms dina, se kuma na koma kan gashi na.
Atleast se da na dauki one hour kafin na gama shafe shafe na, na gyara gashi na na tufke shi da kyakkyawar ribbon silver color, dan shine color da zan amfani da shi yau.
Kaya na dake kan bed wanda na gama yi wa turare na dauko bayan na turare jiki na da na jiki na shiga zurawa.
Dark blue din lace ne da ya ji stone work da silver stones masu matukar tsada, lace din ya hadu matuƙa haka kuma pattern din jikin sa aka cira aka jejjera aka min kan silver net da aka min tai da shi, se ta gefe aka zubo silver net din bayan an bi shi da dinki har baya, se ya bada wani fashion na daban, making me looking more like a bride.
Ana zuwa kan kwalliya kuwa na gyara zama, na shiga rangadawa kai na casual yet classy and fascinating make up, Ina gamawa se gani na fito kamar ba ni ba, kamar dai wata amarya.
Na dauko silver head na hada da dark blue din scarf din lace din na shiga daurawa, kafin kace me na mammalkawaya shi ya fita fit, gaban goshi na na sake gyara gashi na da na kwantar tun ina gyara gashi, looking so ravishing.
Ina gamawa na dauko purse dina na rike, tare da dan yafa silver chantely veil dina da yake purposely for the outfits.
Na dauko heel shoes dina silver color da yasha adon stones na fito zuwa falo na zauna ina daurawa, na saka na kafar dama successfully amma na hagun se ya makale, kuma na kasa gane wai a ina damuwar yake.
Ina cikin kokawa da takalmin na ji unique kamshin sa ba'a Dior sauvage yana ratsa kofofin hanci na, tun ina ji a hankali har na ji yana karuwa, lokacin kam i can't help it dole na dago, dama gashi tun da safe nake auna kamannin sa na yadda possibly ze kasance yanzu, a kan sa na sauke duba na, yana tsaye jikin kofar falo ya tokare da ƙafafuwan sa, yayinda yayi crossing hands din sa a broad chest din sa.
Kasa dauke ido nayi daga kan sa, zuciya ta na racing a kirji na, wani yanayi na musanman na ratsa jiki na, a hankali ya warware hannun sa ya shiga takowa zuwa gare ni, wanda zuciya ta ke buga wa with each takun da yake kara kusanto ni da shi.
Da kyar na iya janye ido na daga kan shi na lumshe ido ina daidaita nutsuwa ta har zuwa lokacin da naji yayi kneeling a gaba na, a hankali kuma naji tattausa kuma faffaɗan palms din sa sun kama kafata zuwa kan cinyar sa, hakan yasa na bude ido batare da na shirya ba na sake zuba masa.
Kan sa na duke yana gyara igiyar takalmin ta baya, kaykkyawar sumar kan sa me taushi da laushi ko a ido a gyare ta kwanta luf se kyalli take yi, ga kuma kamshi da take yi dan kan sa na kasan fuska ta ne.
Ban san ya gama gyara wa ba se gani nayi ya dago fuskar sa, se kuwa na sakin masa murmushi me kyau da ya bayyana haƙora na gaba daya ina fadin
"Welcome back Ya Masdooq".
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...