Ouummey 051
Page 5️⃣1️⃣
_____________________Ina kitchen ina hada breakfast ya dawo daga masallaci kamar yadda na san shi tun ainahi, in aka yi subh baya tahowa se gari yayi haske sosai, Aunty A'i na daki na bar mata shirya twins, dama haka muke yi, in zata yi girki zan shirya su, in kuma ni zan shirya su ita kuma zata yi girki.
Ina gamawa na shiga fita da su zuwa tsakiyar falon dan a nan muke cin abinci, na kai na koma dan kwaso wasu se ganin sa naji tsaye kofar kitchen din ya harde hannuwa a kirji yana bi na da wannan kallon nasa me kashe min jiki tun a da can.
Na dauke kai ina gaishe shi, ko ya amsa to ni dai ban ji ba se hannu da ya mika min, na kalli hannun na kalle shi
"Zan taya ki ne".
Ajiyar zuciya nayi tare da mika masa team flask din hannu na dan bana san jan magana da safiyar nan, shi kuwa na ga kamar ba Ya Masdooq din da na sani ba mata yawan magana yanzu duk waccan matar ta sa ta bata shi da surutu.
Tunanin nan da nayi se ya dawo min da zancen mu na jiya, wai yana nema mata yafiya, kai jama'a!!
Na dauki warmer daya da ta saura dq oat fin twins tare da kokarin daukan cups sedai kayan sun wa hannu na yawa, haka na fita da wadannan da tunanin na kai na dawo, ina komawa na samu ya dauko se na juya zuwa falon ya biyo bayana.
"Bari naje nayi wanka, na je?"
Ya fadi yana kallon na, wani yanayi na can shekarun baya ya dawo min, a lokacin duk abinda ze fada min se ya faɗa da sigar tambaya, har na taba ce masa me yasa yake haka, amsar da ya bani a lokacin itace wai saboda hankalin sa na kwanciya da yin koma me ne in ya san da amincewa ta.
A hankali na dube shi, idanun sa na kai na se na wa da suke taf da hawaye suka fada cikin nasa, ya langwabar da kai yadda ya saba min a da in yana lallashi na, se kawai hawayen nan suka shiga zuba kamar an koro su, dan sanabe se ga shi har da shessheka, shima na sa idanun sun kada, da alama shima bayan ya tuna, ya kama hannaye na ya rike cikin nasa tare da ja na jikin sa ya rungume yana cewa cikin raunananniyar murya
"I miss my Barbie, I miss my Honeybun, her cute smile, her magic eyes, her melodious voice, her...her...her everything, I miss you AIMAAAAHHHHH".
Nima hannu na saka na rungume shi kam kam, Ina jin na fi shi wannan kewar da yake fadi, kewar Ya Masdooq dina, my sweetheart, my sweet tooth, my friend, my besty and my other half, a yanzu ba batu ne ake yi na miji da mata ba, batu ne ake yi na wancan lokacin da muke Abokai, aminai kuma mafi shakuwar yan uwa, shiyasa na aje komai na tarye shi ɗan nima ina bukatar jin shi cikin jiki na.
"I missed you more, so...Soo...very bad sweetheart, life has been very dull, blank, empty and baadd without you and your care, please don't ever leave me sweetheart, don't pleassssseeee".
Na karasa Please din ina sake fashewa da kuka, se ya zaro ni daga jikin sa ya haɗa fuskokin mu tare da cupping face na, yace cikin irin wancan muryar ta sweetheart dina, tone din da shi kadai yake amfani da shi a gare ni, haka shima wani kadai yake wa magana da shi yace cikin whispering muryar sa very cool
"I won't Barbie, I promise you I won't, and am sorry for leaving you at that time, am sorry and forever will be, u missed you beyond your expectations, beyond words can I explain, don't leave me too Barbie, never please".
Gyada mai kai na shiga yi har lokacin hawaye na basu tsaya ba kamar an bude famfo, ya sa hannu ya lakato ya kalla se kuma ya lumshe ido yace
"Close your eyes".
Ko a da da ban fahimci feelings dina toward him ba bana masa musu balle yanzu dan haka na ja idanu na na rufe, ban san abinda ze yi ba kenan da ban rufe din ba, ga shi kamar aikin asiri na kasa motsa ko da yatsun hannu na ne balle kafafu na balle jiki na gaba daya.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...