Ouummey 003
Page 3️⃣
__________________"Dalla rufe min baki ki saurare ni dan ba gaisuwar ki na kira in ji ba, yanzu haka Mama na kwance a gadon asibiti saboda bakin ciki da takaicin ki, wallahi duk kika sake wani abu ya samu mahaifiyar mu saboda ke ki kuka da kan ki dan se na tabbatar na wulakanta ki, shegiyar yarinya me zubin mayu, kuma wallahi ko da wasa na samu labarin kin zo gidan ko kuma kin kira ta a waya se na kusa kashe ki, tun da kin ce ke bakya jin magana kuma ba'a isa a saki ba to ki nemi wasu yan uwan, dan ko da wasa kada ki sake ki kuma tuna kina da wani dan uwa me sunana, bani wayar nan Yaya Salman".
Naji Muryar Ya Najeeb bayan yaya Salman ya gama nasa, be jira komai ba kuma ya mika masa shima ya dora nasa, daya bayan daya haka yayye na uku suka tabbatar min da babu su babu ni, tare da kashedi me tsauri kan mahaifiyar mu da kuma zuwa gidan mu, Yaya Ahmad ne kadai ne be sanar da ni ya yafe ni ba, ya dai min fada cikin nutsuwar sa kamar yadda ya saba, ya kuma min nasiha a karshe, kafin Ya Salman ya karba ya sake zage ni tas.
Ban ma san ya kashe wayar ba tsabar nisa da nayi cikin tunanin irin rayuwar tashin hankalin da nake ciki, babban abinda yafi damuna a lokacin shine jin Mama na kwance a gadon asibiti hawan jinin ta ya tashi, hawan jinin da ta same shi a dalilina yanzu gashi ya kuma tashi a dalili na.
Anya kuwa akwai mara Sa'a a rayuwa kamar ni? Anya kuwa akwai wadda rayuwar ta bata da wani amfani da ma'ana irin tawa?.
Kuka nake, kukan fili da na boye, zuciya ta na zafi raina na kuna, ina tur da Allah wadai da halaye na na baya, ina kuma kukan rashin samun dama ta biyu wajen iyaye na da yan uwa na, rashin bani damar bayyana musu canji na, rashin bani damar bayyana musu nadama ta, kukan da ban san yaushe zan daina ba.
Ban ankara ba se kiran Sallar Isha na ji, sedai yadda jiri ke kwasa ta kaina na juyawa yasa na kasa tashi balle na gabatar da sallar, har wajejen karfe goma ina nan wajen a yashe, tun ina jin motsin kai kawon Sa'adah har na ji shiru, har kuma lokacin ruwan hawaye sun kasa kafewa daga idanu na, wanda na san da suna karewa da tuni nawa sun jima da karewa dan irin kukan da nayi shekaru biyar baya zuwa wanda nake yi yanzu Allah ne kadai ya san shi.
A hankali na kokarta na tashi zaune tare da gyara zaman lafayar kaina na tada sallah daga zaunen, a haka na gabatar da Isha dan in nace zan mike bana tantamar irin kayin da juwa zata min.
Waya ta da ta fadi gefe na tun sa'ilin da ya Salman ke min zagin karshe na jawo na duba lokaci, karfe goma da hamsin da biyar agogon wayar ya nuna, idanun na kuma suka sauka kan power bank din wayar da ya bayyana saura 2% kawai da nasan ko yaushe zata iya mutuwa.
Da taimakon Allah na mike zuwa bedroom din na bude toilet tare da wanke fuska ta na kuma tara hannu na shiga shan ruwa ba kakkautawa dan irin yunwar da nake ji jikina har wani kakkarwa yake, yana daya daga cikin abinda duk wani makusanci na ya sani rashin jure yunwa ta, sam bani da sauki ta bangaren abinci, ina da saurin jin yunwa kamar kuma yadda bana iya jure ta, yanzun nan se in fita a hayyaci na, akan haka mun yi yawon asibiti sosai da Mama da Abba sedai amsar daya ce, lafiya ta lau kawai halitta tace a haka.
Seda na cika cikina da ruwa sannan na fita, se kuma nayi tsaye ina karewa gadon kallo, tashi daya idanuna suka kuma cika da hawaye, wani shuɗaɗɗan al'amari na dawowa cikin kwakwalwa ta da idanuna.
Ban manta ba, kamar dai war haka dan lokacin ze kai sha daya ko ya haura kadan, na fito daga wanka daure da karamin towel din da be gama ratsa ni ba, kasancewar ina da matukar jin zafi yasa ban yi tunanin saka kaya ba, na fada kan sabon bed dina dake amsa sunan na aure ba daure da towel dina zuciya ta na fada min ai baze yi gangancin shigo min daki ba dan be taba kwatantawa ba, lokacin satin mu biyu da aure, sedai cikin bacci na da a lokacin yayi min mugun dadi dan ta ko ina iska ratsa ni take yi kawai na fara jin wanzuwar wasu sababbin al'amura cikin jiki na, tsananin firgitar da nayi ya sani kasa shaida shine muka shiga dambe, duk yadda yake fada min shi ne ban fasa kokawa da shi ba dan a lokacin na tashin hankali na nunkuwa yayi dan babu abinda ya fado raina face alkawarin da na daukawa muradi na na kin mallaka wa kowa kaina face shi, wannan yasa na kasa fahimta da jin lallashin sa gare ni har ta kai ga yasa min karfi ya karbi abinda yake hakkin sa kuma mallakin sa, wadda se da yayi nadamar da baki baze iya misalta ta ba dan kuwa komai ya sake rincabewa ne bayan faruwar wannan babban al'amari.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...