PAGE EIGHT

193 9 0
                                    

Ouummey 008

Page 8️⃣

___________________Karfe sha biyu da rabi na fita na dora girkin rana, ina cikin haɗa kayan girkin ne kuma Sa'adah ta shigo, bowls din da na yanka veggies din da zan yi amfani da su wajen hada fried rice din ta daga ta juya se kuma ta aje tana jan tsaki

"Mtswww, da Allah kar ki kuma yanka min veggies a cikin wannan bowls din, ban da mugunta ai kin san ba kayan aiki iri  haka bane".

Daga mata kai nayi alamar to kawai dan fikewa fitina na cigaba da aiki na, ta gama ta fita ta dawo ta ce ma balbalawa cooking pot wuta ina neman cutar ta na kona mata saboda bakin ciki, nan ma hakuri na bata kawai, ta dawo tace na kure gudun gas dan rashin tausayi, a nan ne kuma na mata banza dan na san ai shi dai gas me gidan ke siyowa ba ita ba.

Kafin na gama girkin nan ta yi sawu fiye da ashirin cikin kitchen, kuma ko yaushe se ta samu abin fada, kunkuni da harare harare kuwa ba'a magana, dan ina jin ta kasa ƙasa tana fadin ba ze yiwu mutum ya kasa zuwa da kayan kitchen dan rashin gata ba,bita kuma diya me biyayya iyayen ta su siya mata kuma a kashe mata.

Tun da na fahimci so take na tanka se na bawa babu ajiyar ta, ban kuma duban ta ba har na gama na kai kan table na jera, na m gidan kuma na zuba a warmers din da nake ganin sun dace na hada masa basket, kana na koma daki na yi wanka.

Ina fitowa na canja kaya na fito falo na dibi abinci na isasshe, hankali na kwance sanin yanzu zan dinga ci ina koshi.

Da yamma ma haka na shiga kitchen na yi girki, kasancewar na kwana biyu rabo na da tuwo yasa na tuka tuwo shinkafa abina, na daure cikin leda yayi fari tass tayi kyau, gefe daya kuma na hada masa baza miyar taushe na da taji gyada da tantakwashi, ban da naman kaza da na zuba, se na hada banana milk shake dan Ina son sa sosai, na saka a fridge.

Ina aikin na ji dawowar megidan, be neme ba haka nima ban yi karambanin zuwa dakin sa ba, lokacin da na gama ana kiran magrib na fito dan wucewa daki, daidai lokacin shima ya fito dan tafiya masallaci, na dan dukar da kai kasa na masa sannu da zuwa.

Yanzu ma be kalle ni ba bare ya nuna ya san da mutum ma ya sa kai ya wuce fujsar sa ma'abociyar kamala a hade tsaf, na girgiza kai nima na wuce.

Ina idar da Sallah na yi azkhars dina tare da cigaba da lazimi har aka kira Isha itama na tashi na gabatar, ina idarwa da na gama addu'o'i na se na tashi na karawa jikina turare kana na fita dan cin abinci dan naji shigowar maigidan tun dazu.

Ko da naje ba sa kan dining, na ja kujera na zauna tare da lumshe idanuwana, ina a haka na ji bude kofa tare da fitowar su, na ɗan bude ido kadan na bi su da kallo, daga dakin Ya Masdooq din ne suka fito tare suna dariya, da alama dai wani abu n ya basu nishadi.

Lokacin da suka zauna se na tashi na bude warmers na shiga serving din shi, duk da dazu ya nuna baya so amma be sa na zuba ba sedai kirji na na ta duka kar ya gwale ni yanzu ma.

Ina gama zuba komai na fara mikawa gaban sa, dai dai na dauko bowl din coslow zan ake masa ya mike tsaye zumbur kamar wanda aka tsikara cikin ɓacin rai ya kai wa table din gaban mu duka

"Nace ki yi serving dina ne?, Me yasa ke kam ba zaki taba hankali ba a rayuwar ki?, Dalla kwashe wannan haukan naki daga gaba na, daga yau kuma bana bukatar hannun ki wajen zuba min abinci, Sa'adah will be serving me day and night, I mean everytime".

Kasake nayi ina kallon shi, yanzu duk wannan ɓacin ran har da su dukan table dan kawai ba ya san in yi serving din sa ne? Ai da tun farko se yace min baya so kawai, ni kuma I'll respect myself ba zan yi ba, ko da yake na lura kawai neman abinda ze disgani gaban matar sa yake ya kuma bata min rai, dan tun a baya ya san na tsani gwaliya.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now