Ouummey 026
Page 2️⃣6️⃣
____________________Duk da halin da yake ciki haka ya zauna lallashin mu da kwantar mana da hankali kan ba abinda ze faru se khair insha Allah, duk abin nan fa karfin hali ne kawai yake yi dan shima in dai ka san shi kana ganin sa zaka san yana cikin tashin hankali.
Haka ya sallami Ibrahim ya tafi mu kuma muka cigaba da zama cikin zulumi, duk da ni se kwantar min da hankali yake yi tare da ja na da wasa, a haka muka yi sallar Isha mu ka cigaba da zaman jiran Abba.
Aikuwa ten minutes after that ya kira mu a tare, jiki ba laka muka nufi parlon sa, na kama hannun hannun sa na kankame dan shi ne kwarin gwiwa ta, da ace Abba ni kadai ya kira to bana jin kafata ma zata iya dauka na zuwa wajen su.
Shima be hana ni ba, a haka muka shiga ciki, Abba ya kalli hannun mu dake hade ya dauke kan sa ya maida kan Tv, fuskar sa a hade kamar ba Abba na me yawan fara'a ba.
Be wani ja zance ba bayan amsa gaisuwar mu da yayi ya dube ni tare da kiran suna na, azabure na amsa ina zare ido hannu na na rawa, na ma kasa amsa masa se da ya sake kira na, baki na rawa na amsa masa haka ma jiki na, jin haka Ya Masdooq ya sake matse hannu na cikin nasa, hakan kuma ya taimaka wajen ara min ƴar nutsuwa.
"Allah ya kawo mu cikar wata bakwai kamar yadda sharadin mu yake, gashi kuma har yanzu shiru ba wani labari".
Na kasa magana, se girgiza kai da nake yi, fiye da minti biyu kafin na fisgo murya ta
"Abba dan Allah ka kara mana lokaci, wallahi...".
"Ai babu wannan zancen dan bakin alkalami ya riga da ya bushe Nu'aimah, Masdooq".
Abba ya tare ni tun ma kan na karasa, kana ya karashe da kiran sunan Yaya da kan sa ke duke, ya amsa a hankali, muryar sa ta sake yin sanyi fiye da baya
"Yaya makomar alkawarin mu da kai?".
"Yana nan Abba, sedai ina neman alfarma dan Allah".
Girgiza kai Abba yayi,
"Ba halin ka ba ne karanta, kar ka fara, kai din babban mutum ne da aka san ka da magana daya, kar ka canja mana, and well, am sorry to say babu alfarmar da zan iya yi maka ko ita yanzu, ku tashi kuje".
Hakuri Ya Masdooq ya bawa Abba kana ya tashi kamar wanda kwai ya fashewa a ciki idanun sa sun sake rinewa, ni kam kasa tashi nayi se da ya mikar da ni, a jikin sa na jingina ya sa hannu ya rike kafada ta jin yadda jiki na ke rawa ta yadda kafata ma rawar ta ke yi, kuma in yayi gangancin saki na faduwa zan yi, a haka muka fice wanda idanun Abba na kan mu har muka fita kana ya juyo ya dubi Mama da itama din mu take kallo idanun ta cike da wani irin fata.
"Me ke ranki game da hukunci na akan su?".
"Ni kam ina cikin matukar farin ciki da jin dadi, ko ba komai zumuncin mu ze kara karfi, Aimah kuma ta samu abokin rayuwa managarci, alhamdulillah". Mama ta fada cike da farin ciki
"Above all that, tarbiyyar ta ze gyaru, ina hango gyaruwar barakar da muka samar a tare da ita".
"Insha Allah".
Mama ta amsa Abba da ya fadi statement din sa cike da rauni, Abba ya gyara zama ya shiga kiran wayar Baba, ita kuma Mama tana kiran Hajiya Yayah.
Mukam da muka fita be sake ni ba se da ya kai ni bedroom dina ya zaunar da ni a bakin gado na, shima ya zauna gefe na, dukan mu muka yi shiru mun rasa abin fada, ni kam zamewa nayi na kwanta kan bed din ina jin zazzabi from no where na neman rufe ni, har kuma lokacin jiki na be bar rawa ba.
Mun jima a haka sannan ya dago cikin dasasshiyar murya yace
"Am sorry Barbie, I've failed, na kasa tsaya miki, na kasa baki farin ciki, am very sorry".
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...