Ouummey 040
Page 4️⃣0️⃣
_________________"Na taba ce miki na daina son ta, ko na taba fada miki yanzu bana son Aimah?, Me yasa kike neman complicating issues ne?".
Kalaman sun doke ta matuka, sun kuma shige ta yadda bata taɓa zata ba, bakin ta ya shiga rawa kamar wadda aka tsoma a kankara
"Kana son ta ke nufi?, So kake kace min kana son ta har yanzu?".
"Ban taba ce miki bana san Aimah ba balle ki titsiye ni da maganganu haka, this is unlike you Sa'adah, na roki da Allah kar ki canja, kar ki kawo matsala cikin rayuwar auren mu".
Gaba daya hankalin ta baya kan pleading din da yake mata, abu daya kunnen ya ya jiye mata kuma akan shi take magana dan haka ta dora
"Despite a that happened in the past?, All the heartbreak, all the denial, amma kake son ta har yanzu?".
Se da ya sha mur ganin tana neman kawo masa wata maganar banza
"Koma me ya faru a bayan is none of your business, Abu ne da ya shafe ni ni da Aimah, babu abinda ya shafe ki balle ya kawo sunan ki ciki, and am warning you for the first and last time, kar ki sake, kar ki ƙara, kar ki kuma yi min katsalandan cikin rayuwa ta, in zaki yi magana da ni kiyi ta abinda ya shafe ni ni dake amma ba ni da Aimah ba, na Shata miki layi ina kuma umartar ki da ki kiyaye tsallake shi, in ba haka ba tabbas zaki kuka da idanun ki".
Daga haka ya wuce ya dauki trolley din sa ya ja ya fice fuuuu, ta bata masa rai, wallahi ta bata masa rai, be taba zaton haka daga gare ta ba, a yadda yake ganin ta ya kuma dauke ta gaba daya ta baro wallahi.
Ran sa a bace ya saka kayan a backseat ya koma gaba ya ja motar ya fice daga gidan, bayan ya gargadi gateman kan ya saka ido sosai a kuma kula sosai.
Yana daukar hanyar asibitin ya dinga jin wani farin ciki na tahowa from nowhere yana washe duk wani ɓacin ran da Sa'adah ta cusa masa, ya dinga jin dokin ya karasa ya yi tozali da fuskar ta da ta cute babies din sa.
Yana yin parking ya nemo cleaners suka taya shi kwasar kayan zuwa dakin, yana shiga su Hajiya Yayah suka mike tana ta mishi fadan ya bar su a daki bayan ya san dare yayi, har sun kai bakin kofa ya dakatar da su da fadin
"Ehm ina ganin ba se an je an dauki Sa'adah ba, na yi magana da ita tace zata kwana a gida kawai, kuma na wa gateman magana kan ya kula, so ina ganin ba damuwa insha Allah".
"Ko ba tace ba ai ba inda zata je daukar ta, ina tun da ai kana yin tafiya kuma ta zauna ita kadai ko, bana san shashanci fa".
Baba ya amsa yana ficewa daga dakin, su Mama suak rufa masa baya.
Ba su kai Mama gidan ta ba, gidan su suka wuce da ita dan dare yayi, dana kuma ita kadai ce a ciki se matar gateman da shi da suke zaune a boys quarter.
Sa'adah baki sake ta bi Masdooq da kallo har ya fice, gaba daya se ta sake jin komai ya rushe mata, komai ya kare mata, se ta sake rushewa da kuka tana kiran ta shiga uku, a daren ta kira mahaifiyar ta Aunty Hauwa ta sanar mata, ta lallashe ta da kyar kan zata kira Baba da safe, yanzu dare yayi amma baza ta yarda da wannan rashin adalcin ba.
Ranar saboda ɗorawa kai masifa a nan zaune a falo ta kwana, da kyar ta gyangyada, amma bacci dai me sunan bacci ranar Sa'adah bata samu yin shi ba.
Ana yin sallar asuba ta tashi ta yi ta dawo falo ta zauna ta zuba wa kofa idanu, so take ta ga shigowar sa da kuma yanayin da ze shigo a ciki, ita gaba daya ma kan ta ya cushe, yaushe har Aimah da Masdooq din suka samu privacyn yin wani abu da ze samar da ciki?, Tun jiya take tunanin nan amma har yanzu ta kasa hango mata yadda lamarin ya faru.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...