PAGE FOURTY TWO

541 20 3
                                    

Ouummey 042

Page 4️⃣2️⃣

___________________A haka Dr ya shigo ya tadda mu, ganin lamarin yayi karfi ya sa da sauri ya fita se kuma ya dawo bayan sa nurses na biye da shi, yana zuwa ya karbi wata allura a hannun dayar su yayi min, saboda yadda nake a gigice ban ko ji shigar allurar ba se zafin maganin da na ji, a hankali jiki na ya shiga mutuwa haka karfin da na sa na ta raguwa har ya zama jiki na ya saki a hannun Ya Masdooq.

Ya saki ajiyar zuciya ya maida ni kwance tare da gyara min gashi na da ya barbaje kanq ya dubi Dr

"Dr me yake faruwa haka, se wasu abubuwa take yi kamar wadda ke hauka, dan Allah kar ka ce min ƙwaƙwalwar ta ta tabu, wallahi ba zan iya dauka ba, pls Dr".

Dr ya sauke ajiyar zuciya ya dafa kafadar Ya Masdooq

"Ka kwantar fa hankalin ka aboki na, all will be well insha Allah, sedai fada min ya aka yi hakan ya faru, i mean yaya komai ya kasance bayan farkawar ta?".

Komai da ya faru Ya Masdooq ya sanar masa, yayi shiru yana kallo na, se yace ya Masdooq ya matsa masa, be ja ba ya matsa gefe Dr ya matso wajen fuska ta da hawaye ke gangara ta gefen idanu na, ba allurar bacci suka min ba saboda zata iya haifar min da matsala tun da da kyar aka samu na tsallake siradin fadawa coma, allurar kashe jiki suka yi min dan in dai na fighting din da nake, saboda dinki na ze iya budewa, hakan kuma ze jawo matsaloli sosai.

"I know kina ji na ko Nu'aimah?".

Dr ya fada da wannan muryar ta su da suke kwantar wa da mara lafiya hankali,

"In kina ji na just blink your eyes".

Ya fada sanin bq zan iya yin komai da jiki na ba se after thirty minutes dan ba me karfin yayi min ba.

Kamar yadda yace nayi blinking idanu na tare da kokarin bude baki na, "ina baby na?". Shine tambayar da nake son masa amma baki na yayi nauyi

"Kina son ganin Babyn ki ne?".

Dr ya tambaya bayan ya gama kare min kallo, da sauri na dinga blinking alamun eh, se yayi mutmushi yace

"Za ki ga Babyn ki, but only if you promise you won't fight".

Yanzu ma da saurin nake masa blinking saying I agree with my eyes, se ya juya ga su Ya Masdooq,

"Daga bayanin da ka yi min na fahimci tana cikin firgici rashin ganin cikin jikin ta ko in ce Babyn ta, haka kuma akwai tsoro tattare da kalaman ta da kuma idon ta, da na nazarci komai da ka fada se na gane tana cikin tsoron ganin ku, am sorry da abinda na fada, but yess a firgice take da ku, kamar tana tunanin zaku cutar mata da baby, shiyasa take wannan ihun da fadace fadacen, sedai wannan duk tunani na ne, ba wai lallai ya zama haka ba, na riga nayi mata allurar kashe jiki balle na ji ta bakin ta, amma in th next thirty minutes zata sake ta, I'll be here with you guys, three minutes before the time zaku yi hakuri kuyi excusing din mu, ina nufin zaki fita waje dan na samu nutsuwar ta na san Meye damuwar, together with me will be two nurses ga su nan da muka shigo yanzu, hope hakan is okay?".

Masdooq da da yake jin ba inda zashi ya bar wani kato da matar sa su biyu a daki when she's not in her normal Sense se hankalin sa ya kwanta jin da nurses biyu, so se ya daga wa Dr din kai, damuwa cunkushe a ran sa, yanzu in ya zama su din ne Aimah take tsoro bata kuma san gani me ze faru?.

Zuciyar sa na hakalto masa abinda ka iya faruwa sedai yana korewa dan baya jin ze iya yadda da hakan.

As Dr planned, three minutes to the time suka fita gaba daya jiki a sanyaye, Ya Masdooq ne na karshe, kuma ko da yaje bakin kofar se da ya juyo ya kalle mu kafin ya hadiye yawu ya fita, sedai be je da nisa ba, jikin kofar ya ja ya tsaya in case of cases.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now