Ouummey 041
Page 4️⃣1️⃣
___________________"Am sorry to say yar uwar ku na fama da depression".
Dr ya fada yana zuba musu ido dan ganin reaction din su, sedai kamar ba su fahimta na dan duka shi suke kallo ba ko kiftawa
"Aikin da aka mata was a successful one, so a ka'ida ya kamata ace ta farka tun jiya dan alluran baccin da aka mata ba me karfi nace, so ganin har yanzu bata farka ba yasa muka yi running mata series of tests, only to find out that tana fama da depression, and she's at second to the final stage, dan a binciken mu bata dade da shi ba, sedai ya shige ta da karfi ne, da alamar duk damuwar da ta assasa mata ciwon ba kara bace, se kuma shi wannan depression din ya hadu da ciwon nakuda yaso ya taba mata ƙwaƙwalwa, cikin ikon Allah hakan be faru ba amma ta shiga mini coma shiyasa har yau bata farka ba, after being examined by a neurologist ya sanar mana ba zata yi exceeding tomorrow ba zata farka Insha Allah, sedai ba wai dole ne se ta farka a goben ba, she's just suppose to be".
Tun da ya fara bayani Yaya Ahmad da ya karaso yau ya kwantar da kan sa kan table cikin kunar rai, Ya Masdooq kuma ya sunkuyar da kai, the other three kuwa idanun su duk sun kada na tashin hankali.
Dr yayi rubutu a takarda ya tura musu gaban su
"These are the medications da muke bukata now, akwai bukatar a siyo su yanzu".
Hannu ya Masdooq ya mika ya dauki papern ya tashi ya fita daga dakin yana layin tashin hankali kamar wanda ya shawu, gaba daya kan sa ya kulle kwakwalwar sa ta kasa ma yin wani tunani, shi dai yana tafe ne kawai amma he's feeling empty and blank a kwakwalwar shi, yana tafe mutane na ta kallon shi saboda yadda yake hada hanya har ya kai pharmacy din asibitin ya siyo komai ya juyo.
A dakin da aka canja mata ya tadda su Ya Salman da su Hajiya Yayah duka sun rufu kan Aimah, Aunty Luba kuka take yi da kana gani zaka san a dame take, ya Ahmad ma sa'i da lokaci yana kai handkerchief ya share idanu haka ya Najeeb, Ya Farooq da Ya Salman kuwa idanun su sun yi jajir har fiye da na masu kukan, Hajiya Yayah da Mama ma kuka suke , duk taurin ran Hajiya Yayah da taji me likita ya fada se gata tana zubar hawaye riris, balle Mama da se da Ya Farooq ya tare ta saboda baya da tayi zata fadi.
Masdooq ya samu gefe daya ya aje ledar magungunan ya koma jikin bango ya kifa kan sa, only God knows what's going on in his mind, be san adadin lokacin da ya dauka a haka ba, shidai ya san an dafa shi tare da juyo da shi, daga nan shima se kwasar shi aka yi.
Wannan ya dada daga hankalin su, Mama se kuka take yi tana fadin duk ita ta ja komai, da bata yi fushi da Aimah ba da bata shiga damuwa har ta haddasa mata ciwo haka ba, hankalin su be yi kololuwar tashi ba se da yaran suka fara kuka, Dr yace a hada musu madara a basu, amma fir sun ki karbar madarar, anyi anyi sun ki karba, har allurai aka musu amma sun ki karba, daga karshe Dr yace sedai ayi pumping breast milk din into feeding bottles se a gwada basu a gani.
Aunty Luba ce tayi, aka wanke breast din, nurses suka yi sterilizing feeding bottles din sannan aka yi, cikin ikon Allah se kuwa gashi sun karba, yadda suke sha da sauri will define how hungry they're, ba wanda be share kwalla ba dan tausayin su se baban su dake kwance shima ana fama akan shi dan ciwon zuciyar sa ne ya tashi.
Daga Mama har Hajiya Yayah ranar a asibitin suka kwana, Ya Farooq ma ya kwana wajen Ya Masdooq.
Washegari Ya Masdooq ya farka sedai cikin ciwo yake, se Drs suka sake masa allurar bacci dan ya samu ya huta, bugun da zuciyar sa yake ya zarce ka'ida and abun na neman zama out of control, dole ana bukatar ya huta bugun zuciyar sa yayi stabilizing.
Maimakon farim ciki da suke ciki shekaranjiya se ga shi abu ya juye zuwa damuwa, kowa ka gani zuciya ba dadi, Aunty Luba na zuwa ta dauki babies din tayi feeding duk da ba ma su nema ba, amma se gashi sun karba suna ta sha, hakan yayi showing ba wai basa jin yunwa bane kawai ba su da rigima ne, and a wannan part din they resemble Masdooq me, dan kuwa Aimah na yarinya akwai kuka da karadi.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...