Ouummey 010
Page 🔟
__________________Kamar yadda yace mayafi na dauko muka tafi amsa kiran Baba, wato muka tafi gidan su Ya Masdooq wajen mahaifin sa da muke kira Baba.
Duk da nayi mamakin yadda aka yi Baba ya san da matsalar amma ta wani bangare zuciya ta na cike da hope a kan sa, irin son da ya gwada min a baya kamar ƴar cikin sa da yadda yake jiɓintar lamari na ya sa nake jin zan samu adalci a can gaban su.
Se kuma daga baya na daina tunanin yadda aka yi ya san da fadan, babar Sa'adah kanwata sa ce, Sa'adah ta kira ta ta sanar mata, ita kuma shine ta kira Baba wan ta ta fada masa, wannan fa a nawa tunanin ne dan har yau ban san yadda aka yi batun yaje ga Baba ba.
Abinda na sani shine Baba na matukar san Aunty Hauwa Babar Sa'adah dan su kadai iyayen su suka haifa, aka kuma mutu aka bar su tare, shi ya dau ragamar kulawa da ita duk da cewa suna zaune ne hannun kawun su, Baba na matukar son Aunty Hauwa, yana ji da ita kamar me dan yana ganin ita kadai ce jinin sa shakikiya kwaya daya, haka kuma yana ganin ta macece me rauni, shiyasa har bayan auren ta duk abinda take so in ta kira Baba se yayi mata, wannan yasa ma har suka dan fara samun matsala da Hajiya Yayah dan wani sa'in ana take mata hajji wajen neman dole se an mata abinda take so, kafin daga baya su bar garin ita da mijin ta, wannan yasa suka samu zaman lafiya.
Ina wannan tunanin se jin tsayuwar mota nayi, na dago na dubi gidan ta glass ɗin window back seat din da nake zaune, na yunkura ina runtse ido saboda zafin da kafata ke yi, da kyar na fito nayi gaba batare da na tsaya duban su ba, can na bar su sun tsaya yana lallashin matar sa.
Da sallama na shiga falon, Aunty Luba da Hajiya Yayah na zaune suka amsa min, ganin su yasa zuciya ta yin rauni sosai, idanuna suka cika da hawaye.
Na daga kafa a sanyaye na karasa gaban Hajiya Yayah na zube ina gaishe ta, kuka ya kwace min na kifa kai na kan laps din ta ina yin shi, bata hana ni ba haka ma Aunty Luba, suka bar ni nayi shi sosai ta yadda har jiki na dake rawa ya daina, kana na dago bayan na share hawaye na na gaida Aunty Luba, ta amsa min can kasa tana cigaba da feeding babyn ta da take yi.
Se lokacin ina lura ashe su Ya Masdooq din sun shigo ina kuka, na janye ido na koma na sake kifa kai na jikin kafafun Hajiya Yayah, a hankali na ji saukar hannun ya kan baya na tana shafawa alamar rarrashi sedai bata ce komai ba, tsayin lokaci tana min haka har na ji zuciya ta ta fara sanyi na shiga sakin ajiyar zuciya a kai a kai, mintuna kusan biyar kafin ta dago ni ta zuba wa fuska ta ido sannan can kasa tace min
"Kiyi hakuri, ki cigaba da hakuri, shine abinda zan ce miki a yanzu NU'AIMAH".
Daga mata kai nayi, se ta janye ni daga jikin ta ta tashi zuwa sama ta sanar da Baba zuwan mu, suka sauko tare da baban, ya zauna a three sitter itama Hajiya Yayah ta zauna gefen sa.
Murya a dishe saboda kukan da na sha na matsa gaban Baba ina gaida shi, ya dago ya tsare ni da ido na lokaci me ɗan tsayi kafin ya kau da kan sa ya amsa.
Duk da gwiwa ta ta fara sanyi amma dai ban sare ba, na ja gefe nayi lamo kamar wata marainiya, su Ya ma suka gaida shi ya amsa musu cikin fara'a musamman Sa'adah, a kuma lokacin ne naji a raina tabbas adalcin da nake nema ba zan samu ba.Baba bayan ƴar sa ze bi, daga yadda ya amsa min gaisuwa da yadda ya amsa tata na gane hakan, se zuciya ta ta sake karyewa, amma dai na jure.
Gyaran murya Baba yayi ya tambayi Ya Masdooq me ke faruwa a gidan namu? Aunty Hauwa ta kira shi hankali tashe wai Sa'adah ta kira ta tana kuka tama kasa sanar da ita me ke faruwa.
Ya ya gyara zama ya dukar da kai kasa kafin ya sanar da iya abinda ya sani, wato ya dawo daga aiki ya tarar idanun Sa'adah jajir alamun ta sha kuka, ga kuma shatin hannu a kumatun ta na mari, ko da ya tambaye ta me ya faru se ta sake kecewa da kuka, yayi iya yin sa taki sanar da shi komai se kuka da take yi.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...